Malam Ibrahim Shekarau ya lashe zaben Sanatan Kano ta tsakiya

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam'iyyar APC ya lashe zaben shi wanda akayi ranar Asabar da ta gabata.
Da yake bayyana sakamakon zaben, Baturen INEC kuma me karbar sakamako, Prof. Adamu Alhaji-Samaila ya bayyana Malam Ibrahim Shekarau wanda ya lashe zaben bayan da ya samu kuri'u 506, 271, yayin da abokin hamayyarshi, Aliyu Sani-Madawakingini kuma ya tashi da kuri'u 276, 768.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Malam Ibrahim Shekarau ya lashe zaben Sanatan Kano ta tsakiya"

Post a Comment