Namu yayi abin yabo: Dan Arewa na farko daya kafa tarihin da babu irinshi a makarantar horar da Sojoji ta NDA

A bikin yaye sabbin sojojin da akayi ranar Asabardin data gabata a makarantar horar da sojoji ta Kaduna wadda ake kira da NDA a takaice, mutane musamman 'yan Arewa sunga abin birgewa daga wani soja me suna Ahmad Bature domin kuwa duk wata kyauta da ake bayarwa a gurin shine ya lasheta. An rika kiran sunanshi yana tasowa yana karbar kyautuka kuma duk lokacin da aka kira sai mutane sun tafa mai kuma anyi shewa.
Ahmad Bature ya fito daga jihar sakkwato inda a shekarar 2012 ya shiga makarantar ta NDA, ya nuna hazaka sosai ta yanda saida ya zama me horar da sabbin sojoji da aka dauka na ajin farko a lokaci guda kuma yana dalibi, rahotanni sunce yawan sojojin da aka baiwa bature ya kula dasu ba'a taba baiwa wani soja guda ya kula dasuba a tarihin makarantar ba, akwai lokacin da Za'a tura Ahmad wani kwas amma saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajan horas da kananan sojoji saida aka daga lokacin tafiyar tashi.
A lokacin daya kai shekarar karshe ta karatu Ahmad ya zama shugaban dalibai kuma saida akayi butumbutuminshi saboda tunawa dashi da kuma irin gudummuwar dayake bayarwa.
Haka kuma Ahmadne mafi karancin shekaru daya taba rike mukamin shugaban daliban.
Ahmad ya kammala karatu da sakamako mafi kyau a tsakanin dalibai kuma an yabeshi da kyakkyawan hali da tarbiyya da sanin ya kamata.
A tarihin makarantar horar da sojojin ta NDA ba'a taba samun dalibin daya kafa tarihin da Ahmad ya kafaba daga Arewacin kasarnan, muna tayashi murna da fatan Allah ya tsare ya kima kara daukaka.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Namu yayi abin yabo: Dan Arewa na farko daya kafa tarihin da babu irinshi a makarantar horar da Sojoji ta NDA"

Post a Comment