Mun fasa karbar bindigogi daga Amurka- Duterte

Shugaban kasar Philippines,Rodrigo Duterte ya
ce ya bayar da umarnin a soke kwangilar siyan
dubban bindigogi daga Amurka.
Mr Duterte ya ce kasar sa zata duba zabi mafi
sauki.
Fiye da bindigogin Amurka dubu ashirin da biyar
ne ake sa ran za a bawa 'yan sandan Philippines.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai wato
Amurka da Philippines ta yi tsami tun bayan
hawan Mr Duterte kan mulki.
Akwai dai rahotannin da ke cewa Amurkan ma na
shirin fasa kai bindigogin kasar ta Philippines
saboda damuwar da ta ke da ita kan tsauraran
matakan da Mr Duterte ya dauka a kan masu
safarar miyagun kwayoyi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mun fasa karbar bindigogi daga Amurka- Duterte"

Post a Comment