Nafisa Abdullahi ta mayar da martani akan 'Fadanta da Rahama Sadau akan Saurayi'
Bayan da wani shafin watsa labaran fina-finan Hausa ya wallafa cewa, manyan taurari biyu, watau Nafisa Abdullahi da Rahama Sadau sun yi fada akan Saurayi, Nafisar ta mayar da martani akan wannan labari.
Nafisar tace, Da kuna bin yadda ya kamata wajan nemo labarai, na tabbata da kun wuce matsayin da kuke yanzu.
A wani martanin na daban kuma bayan da wata ta tambayi Nafisar wai kunyi fada akan Saurayi?
Sai Nafisar ta bata amsar cewa, Toh ban sani badai, gani na yi kawai, Ni so nake ma in tambaya, Chachan bakine, ko kuma gisha-gishane?
A makon da ya gabata dai mun ga wani rubutun Nafisar da take caccakar wata da ta bayyana a matsayin me kokarin bin samarin wasu duk da tana nuna cewa ita tana da Aji. Saidai Nafisar bata bayyana ko da wa take ba.

0 Response to "Nafisa Abdullahi ta mayar da martani akan 'Fadanta da Rahama Sadau akan Saurayi'"
Post a Comment