YAR MALAM TAKI HALIN MALAM COMPLETE NOVEL

I thank Almighty Allah (s.a.w) who given me opportunity to created&write diz special novels

Special thanks to my  Luvly parents may Allah bless them abundantly

Special greating goes to my sister's and brothers,may Allah bless them
          Alhamduliilah for everything

Misalin karfe 11pm na dare,babu yawaitar mutane a    titin sai kadan_kadan.hasken fitulu kake gani a titi.

Wata yarinya na hango kamar balarabiya saboda kyawunta very beautiful.

Sanye take da purple gown  mai golden stones a jikinta irin ta amsheta sosai, shape din rigar kadai zai tabbatar maka da yanayin rawar kanta.

Farace Sol very white in complexion,ga gashi da hanci,yalwar gashin gira da karamin baki irin pinkish lips dinnan馃拫

Duk gashin kanta bai hanata sanya golden din attachment ba,kunnenta ta shirya barima kamar hudu ga hudar hanci.

Wata katuwar trolley ce golden a hannunta,tana danna wayarta kirar i phone 7+ da alama calling wani takeyiii

Wata maroon colour venza ce ta tsaya a gefenta tanayi mata signa alamar ta karaso...

Dogon tsaki ta ja Wanda har na cikin motar yana iya hango tsukan da tayiii

Ya fito sanya yake da wata shadda gezna dinkin babbar Riga farine tas,dogo irin giant dinnan yayi masifar kyau....

"Yan mata sannu fa kinyi kyau wallahi,ko kinsan tsayiwarki nan yana iya haifar d accident pls ki taimakeni na saukeki gida"


Ta kara yin tsaki mtssss"kaga dallah malam ba kainake jira ba,kagane ka ja tsummar kafarka ka wuce ka fahimta banza stupid kawai......

Ya bude baki galala yana kallonta wai yau shi mace ke cewa banza stupid tabdi Jan,ubanta waye a garinnan tasan wayeshi kuwa....

Kamar tasan tunanin da yakeyi ta kwashe da dariya"da kabar bata lokacin ka gurin tunani ni yar wacece ,idan kuma ka cikani da surutu na lahira sai ya fika jin dadi"

Horn din wata bakar Prado suka jiyo cikin hanzari mai driving din motar ya fito yana rawar jiki

"Hajiya Dan girman Allah kiyi min rai wlh yarinyata aka kwantar a asibiti,kiyi min afuwa na bar a tsaye"

Ta murmusa idi driver kenan "bakomai amma dai ka kiyaye gaba" ungo wannan 10k ta bashi ka siya mata magani ka hau napep ka wuce ni zanyi driving.

Ya tsugunna har kasa yana godiya ta shige motar ta bade wannan saurayin da kura....

Shima motarsa ya shige yabi bayanta,driving yakeyi sosai saboda kada ta bace masa.

Cikin mirror ta gano yana bin bayanta kusa d gate din wani Hotel tayi parking.

Shima parking din yayi suka fito a tare,waya ta daga tayi kira sai ga wasu security sun fito daga hotel din,key din motar ta basu suka shige da ita.

Tana girgiza ta karaso gefensa "malam nasan hukunci kazo yimin to gani nan saika kasheni ka huce"

Kasa magana yayi saboda faduwar gabar da ya ji,tayi masa kwarjini sosai a zuciyarsa yace"yanzu duk kyannan da kasaitar nan a hotel zata kwana"impossible ya furta da karfi

Sincerely speaking am really luv u my fans coz kaunarku gareni uncountable ce


Na ga kiranku da messages naku ngd d yadda kuke supporting dina

Honestly nayi littafin nan ne badon cin mutuncin wani ba just yadda fans ke korafin shiru nakiyin new novel,dat y na zo muku d labari mai cike da darasi


     Kubiyoni
             Freshhh khadynku ce

           
Yatsine fuska tayi cikin tsiwa da kisisina take magana"gani nan nasan ka biyoni ka hukuntani ko?to ganinan ka kasheni..."

Tsintar kansa yayi da kasa yi mata komai saboda kwarjininta"tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halacci wannan yarinyar"ya furta a Kasan makoshinsa

Kallon up and down tayi masa tayi tsaki"karamin Mara kunya kawai,kaga ni I have alot to do naga kai baka da abinyi.

Ta yatsina fuska sai dai kafin na bar gurin am mufleeha by name yadda zaka buncikonin ka ji dadin hukuntaniii ta shigewarta ta barshi tsaye.

Gate din yabi da kallo mufleeha ya maimaita hmm sunanki mai dadi and u re so beautiful why halinki ba mai kyauba????

Motarsa ya shige ya hau titi da gudu cikin parking space na gidanshi ya tsaya ya dade yana tunani sannan ya shige ciki.

a falo ya sami meenal tana zaune ta zabga tagumi da gani tasha kuka,da gudunta ta nufoshi yayi mata smiling kadan.

Prince ina ka boye yau inata kiranka kaki dagawa,yayi tsaki meeting mukayii Oga yazo naija ne.

Bayan yayi wanka yayi shirun baccine yaci abinci yayi kwanciyarsa ko ta kan meenal bai bi ba.

******
Shigar mufleeha ke da wuya Room 8 ta shige,straight jikin mirror ta tsaya ta cire karamin veil dinta.

Wanka ta shiga tayiii ta dauro alwala tayi Nafila raka'a biyu tana jero addu'oi tana kuka tana nemarwa kanta shiriya da kuma al'ummar musulmi.

Night gown pink ta sanya,sannan ta haye bed ta kwanta.wayarta ta kunna ta nemo wani contact sweet sis naga ni a rubuce.

da sallama tafara tana murna da farinciki,daga can bangaren aka amsa cikin muryar bacci.

Cikin fada wadda mufleeha ta kira da sis take fadin"sai mutum yana bacci zaki kira shi,nifa banason halayyarki mufleeha"

Tsaki tayi"ke ni ba wannan ba just nakasa bacci ne yasa nace bari na kira sister ko lfy,hop babu abinda y sami yar kanwata ko?

Yarinyar da aka kira da sister ta kara yin dogon tsakii"aikin banza idan mutum ya dami dani ya dinga zama kusa dani mana ya kuma gyara halayensa"ta kashe wayar

Wasu zafafan hawayene suka biyo kan kumatun mufleeha....a haka ta kwanta bacci barawo ya sace ta.

*****
Sauri_Sauri ya shirya ya nufi office amma tunaninsa guda dayane wacece mufleeha.

Sai yammaci ya tashi,a wani katafaren super market ya tsaya don yayi shopping.

Gurin cosmetic ya tsaya don ya tsiyama meenal dinshi Abu...

Cin Karo sukayii da mufleeha tayi saurin cire bakin glass dinta,"idiot what are u looking for ???mtsssss

Ya dago sexy eyes dinshi"nine idiot?banza kawai Mara kamun kai ji yadda kikayi dressing kamar Christian mtssss Sam baki da halayya mai kyau...

Jikinta ne yayi sanyi sosai duk lokacin da akayi tir d halinta sai jikinta yayi sanyi sosai.

Fasa shopping din tayi tanufi waje bakin motar saurayin nata ta tsaya shikuma ya fito daga cikin motar da Sauri a time din mahfuz ya fito daga super  market din

Subhanallah ya furta"me ya hada big bro da wannan marar kamun kan yarinyar???? Babban yayansa ya gani ya karbar hand bag din mufleeha yana kokarin sanyamata cikin mota

Na sadaukar da littafin ga tauraruwata my little sis ISLAM,may Allah bless her hundred percent I really luv u wit all my hearty

Luv u more swthrt,I can't express hw much I lov you

            Fresh khadynku ce

Wani killer smile tayi lokacin da kallonta ya kai kan Mahfouz..a hankali ya iya karasowa kusa da big bro dinshi.

Wani hug big bro ya kaimishi yana murnar ganinshi,jikin Mahfouz a sanyaye ya mayar masa da smile kadan.

Na kira wayarka a kashe why?sai a time din ya dawo daga dogon tunanin da tafi.

Big bro mai suna Deen yace"babyna ga little Mahfouz fa bro dina inaji dashi sosai"

Mahfouz ta maimaita cikin zuciyarta gaskiya sunanshi akwai dadi sannan ta yatsina fuska "sannu little Mahfouz hop kana lfy kuma everything is going perfect? Ya su hajiya???

a dakile yace normal yana mai mamakinta yadda ta nuna bata taba ganinshi ba,ga kuma mamakin bro dinshi mene ya hadasu da mufleeha?????

Deen ne yayi gyaran murya" uhm lil Mahfouz ga mufleeha nan yarinyar da nake son Aura ta shigo a ta biyu Ina son goyon bayanka a gurin hajiya coz zatace Teema bata dau shekaru gidana ba zankuma wani auren.

Mahfouz ya hadiyi yawun bakin ciki"no wahala bro bari na gangara gida cox I'm very tied bye i will give u a call bro.

Mufleeha tayi murmushi bye our lil Mahfouz Allah ya tsare hanya.... Pls my regard to hajiya.OK Thom ya furta gently.

*****
Sanye take da atampha super Europe Dan a fadarta ta gaji da super England brown and yellow colour.

Dinkin Riga da zani tayi daurinta ture kaga tsiya,takalminta yellow da hand bag din ta yellow, ta sanya sarkarta kirar Dubai irin mai Dan matse wuyannan,babu gyale coz idan ta sanya Atampha a fadar ta mayafi kara nauyi yakeyi.

Cikin takun kasaita ta karaso cikin restaurant din fitinannen kamshinta ne ya ja hankalin mutanen gurin babu mace babu namiji coz kowa nason ganin mai kamshin.

Ganinta kuma yafi kamshin abin mamaki ido hudu sukayi da Mahfouz coz yau meenal dinshi ta tashi da zazzabi.

Kujera ta ja ta zauna, tayi kamar bata sanshi ba waiter taxo ta kawo mata list na abincin ta zabi Wanda takeso.

Ta fara cin abinci ne sukayi ido hudu da Mahfouz ya ja dogon tsakii, harararsa tayi dai_dai lokacin ya zo fita ya biyo ta gefenta ya furta useless a hankali.

Ta dan gyara zama ta daga murya"malam wai kai maye ne tun dazu kakeyimin alamar na baka numberna da idonka ynz kuma ka wani biyo gefe na duk Inda naje sai ka je,to ni ba irin ka nake saurara ba banza gara"

Ta Mike d Sauri ta fice wasu na dariya wasu kuma haushi ta basu,cikin zafin nama ya shige motarsa ya bi bayanta

My mum my everything nice to have u mum馃拑no 1 lyk u sweet mum in diz world, u make my life so sweet馃拑馃拫luv u more馃拑馃拫

Also my Dad my everything nice to have u, luv u more馃拑馃槏

           4鈨�
Gudu take tsalawa kan titi tana saurarar wakar Nancy ajram ta habibana,sai nishadi takeji a ranta cikin wani park ta shige ta jima tana waya daga kasan da kawarta take waya, kuma kawar ma kamar suna da dangantaka ..

Ta fito cikin isa da takama ta karasa bakin pool din dukanninsu kayan wankane a jikinsu ita dayace mai atampha.

Ihu suka dauka wowww one in town baby kina wuta fa,gaskiya kinyi kyau,tabe baki tayii ta zauna kan wani chair gefensu hannu ta daga musu Hiii

Mufeeda ce da yesmin suka koma kusa da ita"babe hw far?yaushe kika karaso naija ne?" mufleeha ta tamvayi mufeeda cikin isa d gadara.

Mufeeda tayi smiling "hmm beauty jiya ne wlh,dat why yesmin ta shirya wannan celebration din"

Mufleeha tayi dariya"babe to mene bayani?ko baki winning bane?

Mufeeda ta kwashe da dariya zo muje kiga sabuwar venza di ta,fara na siya fa...

Wowww babe diz car looking so gud and attractive Allah ya tsare.

Ameen yar malam"cewar wadda aka kira da yesmin ta fada tana dariya.

Mufleeha ta watsa mata wani kallo"designer ki kiyayeni wlh banason rashin mutunci....

Gaba daya suka yi dariya yesmin ta kara cewa "YAR MALAM TAKI HALIN MALAM" wata uwar ashariya mufleeha ta jefa mata"ke ki kiyayeni bana son raini fa"

Afuwan beautyn mu nadaina smile kinji so sorry,gaba daya suka kwashe da dariya banda mufleeha sakamakon ganin Mahfouz na gefen su yana kallonsu da saurarar hirarsu.

"Hmmm kazo Neman gurin zama ne kamar yadda banzan bro dinka yake nema to ba a nan ba,gayyar tsiya arna a eidi ..."

Ya murmusa"look kallon kazama,kucaka,jahila nakeyi miki marar aji kawai kuma nasan bro bai San true colour dinki ba,ni kuma tsakanin shi dani is incomparable coz ni ba sakaran namiji bane dakikiya kawai"

Maza da mata kallon Mahfouz suke suna mamakin da ya iya gayawa mufleeha haka.

Ta karasa gaf dashi"hmmm kasan shi kare kullum burinsa yayi haushi ko ya sami mai bashi abinci,kuma maganar jahilci bana mamaki idan aka kaf danginku babu Wanda yayi sauka sau goma sha biyu kuma ya haddace Qur'an gaba daya da littatafai kamar yadda nayi.

Kuma maganar karatun boko nasan baka samu matsayin masters degree kan addini ba kamar yadda na samu a karancin shekaruna.

Ta zuge hand bag dinta ta fito d ID card dinta,da kuma na lambar yabo a gurin musabaka.

Sannan ta fito d ID card dinta na catering da tayi diploma a harkar girki."kaga ko na fi karfin mutum ya kirani jahila.

Kuma jama'a duk yana haushin nan ne saboda ya nemeni naki amincewa nace masa ina gudun ciwon zamani.....

Hannu ya daga zai mareta tahir babban Abokinsa ya rike,shima ya zo park din a sannan tahir ne da wasu mutane suna rikeshi yana kwacewa zai daketa....

Mota kowaccensu ta shige zasu bar gurin ido hudu tayi dashi yana zubar da kwalla zafin sharrin da tayi masa.

Zuciyarsa a cukunshe sai ya wulakanta yarinyar nan zai ta dandani bakin cikin da ya dandana,ya goge hawayenshi ya fizgi motarsa gudu yakeyi baya ganin gabansa


All diz page 4 u my blood sisi馃槏馃槏luv u Anty fauza irin totally dinnan鉂も潳鉂�
         馃馃馃
Hmmm I really luv you sweet sis馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑

           5鈨�
Driving yake tamkar zai bar garin bacin rai da takaici ne ke addabar zuciyar I know what to do ya furta da karfin tsiya.

Horn yakeyiii da Sauri gate man ya bude mishi katafaren gida Wanda kallo daya zakayii mishi ka tabbatar Wanda ya mallakeshi yana daga cikin millions.

Cikin azama ya fito daga motarsa ya sanya key ya bude kofar falon,kai tsaye upstairs yayi cikin falon ya tsaya cak ganin katon frame mai lauke da picture din mufleeha da Bro dinshi Deen.

Can gefe kuma nata ne guda daya,bakin ciki ya kara rufeshi da ya shiga bedroom gaba daya bedsides din dauke suke da karamin frame din hotunan mufleeha an rubuta true love never end.

Karya ne wallahi ya fada kamar zararre ya janyo wani drawer da gani secret abubuwa ake adanawa aciki,wani karamin diary ya bude.

Page din farko aka rubuta I LOVE YOU MUFLEEHA "yayi tsaki ya tafi next page nan ma kalaman soyyyaya ahaka har ya kai second to d last page nan yaga permanent address dinta da phone number dinta,ganin an rubuta hot line dinta cikin hanzari ya fito da wayarshi ya dauki number din yayi saving.


Hhhhhh dat what I need yayi murmushin samun nasara,well ynx wasan zai fara...yarinyar kin fada tarkona.

Falon kasa ya dawo ya kunna kallo bai wuce 5 minute da zama ba sai ga bro din ya shigo da fara'arsa ganin Mahfouz a guest house dinshi.

Bayan sun gaisa ne Mahfouz ka sanar masa ya zo ya danyi bacci ne wallahi aiki ne yayi mishi yawa a office.

Kana kokari ma lil bro dat y I  like u" daman ina son yau mu hadu gidan hajiya ka tayani rokonta ta barni na kara aure,wallahi bro bana son na rasa mufleeha "

Gaban Mahfouz ne yayi mummunan faduwa amma ya daure"ba matsala but kayi bincike akan halin mufleehar?kasan ance hali wan kyau ne fa."

Hmm lil bro kenan ai ni ko wani irin hali ne da ita matukar va shirka takeyi ba ko kisan kai shine zan ki aurenta kuma ma fa yadda naji yarinyar yar malamai ce,gashi kuma tana da ilimi yar malam ce gaskiya.

Big bro ban gane yadda kaji ba,bakasan iyayen nata bane kana nufin babu wani nata da ka Sani.

Zufa ta karyo masa"tabbas lil bro ban San kowa nata ba hakikanin gsky ban San wani gari take ba ma,bata son mutum ya San garinsu duk cikin kawayenta mutum dayace na ke da yakinin tasan garinsu mufleeha takuma San wacece ita yesmin suna kiranta designer amma kuma ko duniyarnan zaka bata bazata fada maka ba.

Cikin Mahfouz yayi sanyi"big bro kenan zaman kanta takeyii a abuja kenan tabdi wa iya zubilllahi,gaskiya ya kamata ka janye kasan fa hajiya dole su bincika ita da Dad.

Enough is Enough lil bro idan zaka goyamin baya fine idan bazakayi va just keep ur mouth,amma sonta ya zama jinina mufleeha itace rayuwata.

Don't worry big bro ina supporting naka u know I hate ur worry amma ina son idan kana da number din yesmin ka bani na bawa tahir friend dina yasan yadda zaiyi har ta gayamasa garinsu mufleeha.

Hmm zan baka oya take it amma nasan yesmin har ta fi mufleeha taurin kai,amma Allah ya bamu sa'a Ameen Mahfouz ya fada bayan ya gama copy din number yesmin.yayi wa Deen sallama yayi tafiyarsa.
[

Up up mazaje,leaders of tomorrow I'm proud you馃槏.
    May Allah guide u Ameen馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦馃憦

Officers in charge馃憤馃憤馃憤
GALLANT MU GARBA (Daddy)
OFFICER ABDURRAHMAN GARBA
OFFICER MUHAMMAD DUFAILU

     Really luv you my blood brothers Allah y tayaku ruko馃憦I'm proud of u guys馃槂馃拑馃槏馃憤

                6鈨�
Daga bed room ta fito sanye take da night gown doguwa mai dogon hannu maroon colour gashinta a gyare tsaf.

Mufeeda na kallon film din Korea ta mayar da hankalinta sosai kan television din,yesmin kuma tana charting abinta.

Elizabeth house girl dinsu tana mopping ganin fitowar mufleeha yasan Elizabeth durkusa"Good morning ma"

Morning Eli!hop everything is OK"yes ma ta bata amsa sannan kuma tace ur food is ready ta nuna mata dinning.

Okay tnx ta fada ta koma bedroom ta shiga tayi wanka ta shirya cikin shadda wadda akayiwa dinki buba da gani Senegalese ne sukayi dinkin.

To guys Ku tashi muyi break,mufeeda sanye take da sky blue din lace Riga da skirt,yesmin kuma sanye take da English wears Riga da wando"

Mufleeha tayi tsaki"ynx yesmin a haka zamu je kinsan fa shi babban mutum ne kuma abokansa da ke yawan zuwa office dinshi manyane"

Ke malama karki dameni ni fa after dress zan Dora babu kuma nayafinta zan yi using pink hula pink shoe&pink handbag.

Wowww mufeeda ta furta ni kuwa dankwali na zan daura kawai sai red shoe&red handbag...

Mufleeha tayi tsaki nifa dinkin ba dankwali kuma bazansa mayafi ba,rose silk golden zan daura coz shaddar da golden jiki,goldenshoe&golden handbag...

Dariya sukayi gaba daya zamu hadu fa guys,na kallesu kowacce mai kyau ce ta gaske amma ba kamar mufleeha..

Yesmin ta tashi ni fa am OK na koshi fa,Ku hanzarta kunsan evening fly dinmu zai tashi yau dinnan zanvar naija .

Wowww designer ina son US fa kina huta designer ni ko yaushe sai Dubai nake karewa.

Yesmin tayi dariya mufi 2 gwanda ke akan mufi 1 wato mufleeha ita da idan banda Saudi ba kasar da ta taba zuwa, sai shegen tsiwa ga shegen tsoro.

Ta mike da sauri ta rike wuyan yesmin "wallahi y 3 ki kiyayeni kinsan dai nafi karfin kasashen ba Ku kaini kudi da hanya ba,just bana son Hulda da irin turawannan ne gaskiya.

Hhhhhh na manta kinsan yar malam ce,yesmin y 3 ta fada a shakiyanci ita kuma mufi 2 mufeeda kenan zancen banza YAR MALAM ai TAKI HALIN MALAM kinga nima gobe zan wuce malasia ke daya zamu bari gidan nan.

Ta juyo kan mufeeda kamar zata dake ta saboda masifa naji naki halin malam ai wlh duk da Baku San tarihina ba na sami tarbiyar da Baku samu kawai rayuwa tana iya juyawa.

Hmm to ki dakeni mana ace muna zaune shekara uku tare baki taba vamu tarihinki ba ai wlh babu amana tsakaninmu.

Idanunta suka kawo kwalla ta mike ta shige bedroom tana kuka bata son tuna baya bata ga amfanin tuna baya ba.

Wayar ta ta janyo sweet sis hop kina lfy indai ban kiraki va bazaki kirani ba,kina mantawa dani matsayin sister dinki.

daga daya bangaren kuma tsakii yarinyar tayi to me ne dan na manta dake,ke da kika manta da asalinki kina da bakin magana,to ki dawo mahaifarki mana idan kina tare dani kinsan dai duk duniya mu biyu a ka haife mu ko?kinga ina da abinyi kinji yarinyar ta kashe wayarta.

Kukantane ya tsananta daga falo suka jiyo sautin kuka da sauri suka shigo suna tambayarta meya faru?ki tashi mu fita kinji...

Bazani ba kuje kawai ta fada a fusace,lallaminta suka shiga sun San dai itace jarinsu duk matsayin guri idan suka tafi da ita sai mutanen gurin sun sauraresu,gashi bangaren ilimi ita ke fiddasu kunya.

Da kyar suka lallameta ta shirya cikin motar y3  suka fita dan tafi tasu tsada ita bata tara kudi banki kawai ta canza mota shine burinta.

A harabar office din suka yi parking cike da zulumin karbar da za'ayi musu dan sun San bakin rijiya ba gurin was an makaho bane,y3 tace mufleeha ki fara shiga ma biyoki vaya,tsabar haushin da suka bata Jakarta ta fizga ta five ta hau upstairs security suka yi mata ca akai Jakarta ta zuge ta basu 100 thousands ba shiri suka nuna mata hanya....hango wasu security din ta kumayiiii

Aslm gaskiya fans nagode da kaunarku gareni Allahu ya  bar zumunci Ameen馃憦

Thom friends ga number din amma pls WhatsApp only kamar yadda kuka nema a sanya ngd irin da yawa dinnan鉂も潳馃

            7鈨�

daga daya bangaren yarinyar da mufleeha ta kira ta ja wani dogon tsaki"mtsss ke kika Sani ni wallahi banga amfanin kirana da kikeyi ba,kin bar mahaifarki kin barni kuma kinsan mu biyu kacal mamanmu ta Haifa"

Mufleeha taji kuka ya kufce mata I really luv u sistor no 1 lyk u wlh...saurin katseta yarinyar tayi mtssss "nikam ina da abinyi" tayi hanging phone din.

Wani sabon kuka ne ya kwacewa mufleeha hakikanin gsky tana son kanwarta amma kuma ya zatayi ta koma garinsu shine babbar matsalar.

Y3 da mufi 2 suka shigo dakin saboda sautin kukan dasu ke jiyowa daga parlour "babe koma menene just forget ki tashi mu wuce" cewar y3.

Ta kallesu rai a bace bazanje ba Ku tafi kawai,mufi 2 ce ke ta rarrashinta dan gaskiya mufleeha fitilar ganinsu ce.

Ko wani guri ne indai da ita da wuri ake saurarensu,gashi ta bangaren ilimi ita ke fitar dasu kunya su kam suna yinta hundred percent.

a haka suka lallameta ta shirya cikin motar y3 suka fita coz yesmin bata tara kudi a banki burinta yawan canjin motocin da duniya ke yi dasu.kunji shegiya kamar duniyar matabbaciyace馃ぃ.

a harabar office din suka parker jikinsu duk yayi sanyi"gaskiya mufleeha ki fara shiga yadda ta kasance sai mu karaso"cewar y3

Dogon tsaki ta ja,sannan ta dauki hand bag dinta ta wuce upstairs securities ta gani suna ta zazzara ido.

Kai tsaye ta nufi gurin suka tambayi ina pass dinta Jakarta ta bude ta zaro rafas na dubu Dari ta mika musu"I don't have pass but I have diz"ta nuna musu kudin shegun gari ganin kudi suka fara fadin abeg just enter.

 Nanma wasu securities mata ta gani da farko suka ki amsar kudi amma daga baya suka amshe suka bata wani Abu ta shiga dashi.

Wowww beautiful ta fada lokacin da ta shiga ciki amma fa a zuciyarta.

Yayi saurin dagowa jin zazzakar muryarta,ga sansanyan kamshinta uwa uba kyawun halittarta.

Have a sit ya fada ya cigaba da rubutun shi ita kuma mufleeha ta daga wayar mufi 2" ke gamu waje security sun hanamu shiga"

Thom Ku vani 10 minute zankiraku,time din ya kuma satar kallonta ya kauda kai dan shima iya hadu ya hadu ga yayan banki kuma.

Ta gyara zama"pls sir mune Wanda kamal yace zamuxo muna son adinga yi mana odar kayannan"

OK mufleeha ko?u re welcome ya kira wani mai aiki sannan ya kalli mufleeha me zaki sha?am OK sir ta fada a sanyaye ya lura kamar ta ji kunyane kawai ya sanya Peter ya kawomata abubuwa.

Ya miko mata wani littafi gashi ki karanta rules din,ta karba a nutse. Time din kiran y3 ya shigo"ke wai kin manta damune"

Ta kalleshi kallo mai Jan hankali plsss sir ga sauran sun karaso,yayi shiru kmr bazai magana ba saikuma ya kira security a waya.

Bayan sun shigo kowacce hankalinta na kanshi,mufleeha ta mika musu book din suka karanta sai kuma ta kalleshi"sir babu discount gsky is very expensive za mu iya business dinnan kuwa.

Zaku iya mana ya fada a takaice,gaba daya a tare suka mike Thom sai mun shiryo.OK kawai yace dasu har sunkai kofa sai ya furta "mufleeha I need to talk to u"

Ta dawo a sanyaye sukuma suka fice"pls ina son number dinki idan bazaki damu ba"wayarshi ta amsa ta sanya masa.bye tace dashi kawai ta fice.

Suna isa gida har tsalle sukayi kowacce sai murna takeyi nikuwa nace menene nufinsu oho馃槼

Where are u guys鉁�
Amina(momy)馃槏
Fatima(teema)馃槝
       Luv u forever鉂�

Diz page naku ne Ku kadai luv irin totally dinnan鉂na tare馃

             8鈨�
Bayan sun shigo kowaccensu hankalinta na ganshi gaskiya yayi ba karya,guri suka yiwa Kansu su ka zauna shiko hankalinsa na kan mufleeha.

Ta mika musu book din sun karanta amma ba wani understanding su kayi ba,mikewa su kayi a tare mufleeha ta fara magana cikin sanyi"thank u sir sai mun shiryo but babu discount cos is very expensive "

Bakomai mufleeha in kun shirya Ku xo sai mu ga wani kaya ya kamata Ku fara odarsu godiya suka yi masa har sun kai kofa ya furta "uhm bakiji va mufleeha"

Su mufeeda suka fice ita kuma ta koma"pls ina son number dinki"ya fada a takaice...bata bashi amsa ba ta dauki phone dinshi ta sanya mishi hadi da mikewa tsaye bye ta fada in a very cool voice....

Murmushi yayi mata take care of ur self kinji,Thom na gode sir.

Suna zaune falonsu sai murna sukeyii Niko nace shi kuma wannan mene target dinsu a kanshi oho馃し馃徎鈥嶁檧

Misalin 5 suka wuce airport rakiyar yesmin Y3 zata wuce Dubai, sai kusan 7pm suka shigo gida.

Washe gari kamar 8am suka kara fita airport rakiyar mufeeda zuwa America US,sai kusan 2 ta shigo gida.

a parlour tana zaune ita kadai Elizabeth ta shigo hannunta dauke da trolley zataje gida Lagos babanta ba lafiya,50k ta bata sukayi sallama.

Gidan yayi mata tsit wasu hawaye suka gangaro kumatunta hakika mutum Rahma ne gidan va dadi.

Ita ma shiryawa tayi taja trolley dinta ta shige mota maigadi tayi sallama ta wuce hotel.

Tana kwance wayar ta ta shiga sautin kida a gajiye ta dauki phone wata zazzakar muryace ta doki kunnunwanta.

Sunana Umar Faruq nine mai company din da kukaxo daxu,mufleeha hakika kinyimin kuma inasonki da aure dafatan ba ayi wa wani promise va.

Gabanta ne yayi mummunar faduwa ta dan daure"wow nyc name u re welcome ba'ayiwa kowa  promise ba"

Okay tnx ynx kina gida ne?ta dan yi jum "Aa bana gida" kina ina to?ina sharaton hotel....subhanallahi ya gigice sosai mufleeha ya akayi haka shikenan ni bazan samu Matar arziki da zan aura ba????kema haka kike...

Kawayena ina sonku馃槏馃槏

My Rash(bestyna)
My zee dita
My Ruky
Shamsiya sokoto
Fresh fatyna
Danpillo tawa
Amina mother
My Siyama Ummi
My sadiya
Zee bauci
Ummi Kaduna
Luvly Smarsher
       Luv u irin sosai dinnan馃

            9鈨�
Gumi ne ya wanke mata fuska ta fara dana sanin gayamasa,matsalarta daya bata iya karya ba.

Bakomai ngd zan yi kokarin cire ki a zuciyata kinji amma pls ki gyara halayarki domin wata rana uwa ce ke yana kokarin kashe wayar.

Plsss farouq wlh ni kadai ce cikin dakin babu kowa is no what u thinking pls kaxo ka duba ka gani wallahi na rantse maka.

Hmmm ni zaki rainawa hankali amma bari naxo ynx na tabbatar,driver ne ya kawo basu 10 minute suka karaso ba room din ya nufa.

Straight toilet ya bude ba kowa har labulaye ya daddaga ya leka kasan gado sai ya koma bakin kofa "mufleeha kin rainani ko?shine kika kori mutumin kafin nazo ko?"

 Kuka ta fara tunda ba ka yarda dani ba just go karka kara kirana ka mantani cikin rayuwarka ka kyaleni"ta karasa maganar cikin tsawa...

Kofar ya rufe da karfi ya fice wai yau mace ke yi masa ihu haka koma dai meye shi ya jawa kansa.

Da sassafe takira su mufi da yesmin ta gaya musu fada suka fara yimata kin bata mana plan.

Ashe shi wannan kamal abokinsune shike shiga ya fita y gano shegun masu kudin dake Abuja especially wadanda ya Sani.

Umar farouq nutsatsen mutum haifaffen abuja ne shi kadai yake gurin iyayensa,kuma suna da companoni yaje America ya karanta business har yayi PhD nasa.

Yana da ji kai ba ruwansa da harkar mutane kuma ga kyau Allah ya bashi,shine kamal ya tura su gurinshi wai ya San daya daga cikin su zata rudeshi daga su ci kudinshi.

 Saboda yadda ake zuzuta musu shi da farko sunyi tsoron zuwa ma.

Yesmin tayi tsaki"mtssss ni ynz na sami damar da farouq zai ce zai aureni ai wallahi na bar zaman haka to ko me nake samu ynx nasan zai bani fiye dashi kina kwafsa mana sai kiyi ta zama"tayi hanging phone din ta.

Ta kara kirana mufi har sau uku taki yin picking coz taji haushi a karo na hudu ta daga" kinga malama kar ki dameni saboda sokonci kice masa wai kina hotel kuma alhalin kamal ya gayamiki mutumin kirkine,shine kikayimana bakin cikin abinda zamu samu"ita ma hanging phone din ta yi.

Mufleeha ta rasa me ke yi mata dadi ta juya ta kira phone din farouq amma ina ya sanya ta a blacklist.

Ta juya ta kira kamal ya rufeta da fada don tuni su yesmin sun gayamishi zagi in zaga sukayi dashi ya kashe wayar sa.

Ta koma ta kirawo sistor dinta ta daga"pls mufleeha karki kuma kirana kinji ni na mance dake matukar baki dawo mahaifarki ba,naga alama idan kina bugene sai ki kirani ki rainamin hankali"

Subhanallah sistor an gayamiki ina shan wani abune?just keep quite dan naga ba a hankalinki kike ba inji kanwar tata.

Wani gunjin kuka ta fashe dashi hakika zaman lafiya yafi zama dan sarki馃ぃ

Wani message ne ya shigo( luv u wit all my hearty mufleehana Allah y tsareminke daga bakonki na alheri)bata San number din ba amma text din ya burgeta

Deen ta kirawo suka sha fira har take tambayarsa ko shi yayi mata text yace Aa.

Hmm Mahfouz ne ynx was an zai fara zamuga wani mataki zai dauka akan mufleeha???

📿📿📿📿📿📿
         📚📚📚
      📿📿📿
   YAR MALAM👳‍♂
       TAKI HALIN MALAM
                  Na
💍fresh khadyyyy

Ina alfahari dake👍👍👍

Fresh Ummie xeey Abakson
     Marubuciyar a daliln Matar uba,a dalilin so...

Baki bazai iya furta yadda nake sonki ba only thing I know I luv irin sosai dinnan😍😍😍😍🤝😘

             🔟
da sassafe ta shirya ta harhada kayanta ta dawo gida,kitchen ta shiga ta shirya break a gurguje.

Parlour ta dawo ta tarar da wayarta na ringing babu suna number saurin ajiyewa tayi,can kuma sai ga message (morning my Angel,shugaban taurarin duniya God protect u my Angel)

Hmmm murmushi tayi kayi ka gama jiyama ta gane number da ita akayi mata text,kowane ne ma ba ruwanta ita kam.

Bayan ta shirya cikin maroon din lace and silver tayi kyau sosai,sake ficewa tayi bata tsaya ko ina ba sai guest house din Deen.

Tayi rashin sa'a kuwa ta tarar da Mahfouz yaxo binciken da ya saba,a falo ta tarar dashi ..smiling ta tsinci kanta da yi mishi.

Ya hade rai sosai"ke uban me kika zo yi nan"ta bata rai gurin mijina nazo.....hmmm anyi asara dai,daga can ana nan.

Is enough dallah MALAM bani hanya na shige dan kasan babu inda akayimin iyaka banza wofi useless...

Wani gigitaccen mari ya  zuba mata Wanda ya sata saurin gigicewa"ni ka Mara ?"

Na mareki na mari banza kuma matukar baki daina zagi na ba duk sanda muka hadu zaki dinga karbar wannan hukuncin.

 Hannu tayi saurin dagawa zata rama ya murde hannun har wani kara yayi ihu ta sanya wadda har shi kansa sai da ta basa tausayi sosai.

Zubewa tayi akan kujera"banza wawa wlh sai kasan ka mareni azzalumi kawai"tas saukar wani Marin ta kuma ji a kumatunta.

Tabdi Jan hakika ka aikata mummmunan kuskure a rayuwarka zaka ga sakamakon aikinka.

Tana kokarin fita Deen ya shigo "my sweety" ganin fuskarta a kumbure tana kuka ya sanya shi gigicewa

Me yafaru plssss?waya tabaminke sweety na?cikin kuka tace kuma na Fasa aurenka,wannan banzan bro dinka ne ya rufeni da duka ni ina ganin ya karyamin hannu wai dan na tambayi kana ina?

Bai jira ta karasa maganar ba ya shige parlour lafiyayyun mari sau biyu ya wanke fuskar Mahfouz dasu"stupid kawai "yana huci

ta karaso falon kuma yace matukar ban rabu da kai ba sai ya sa anyi min duka,kuma ni gaskiya na hakura dakai....wani sabon mari ya kara kife Mahfouz dashi " mutumin banza to me tayi maka,yanxu na gane Ashe baka son farincikina oya get out of my house kada kuma ka kara zuwa"

Gwalo tayi masa ganin yadda yake huci kamar zai rama,harararsa ta yi ta gefen ido saurin ficewa yayi.

Deen ya durkusa kasa yana ta bata hakuri har ta sauko daga yake cemata next week zai xo ya dauketa zataje gaida hajiyarsa,saurin bata rai tayi ita kam bazata iya aurensa ba gashi kuma taga shi da gaske yake.

Smiling tayi Allah ya kaimu swthrt...Ameen ya fada cikin tsananin murna.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

1 Response to "YAR MALAM TAKI HALIN MALAM COMPLETE NOVEL"