Asalin Atiku Abubakar dan kasar kamaru ne

A karshen makon da ya gabatane shugaban masu rajin kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ba dan Najeriya bane, dan asalin kasar Kamarune, wannan lamari ya jawo cece-kuce musamman a shafukan sada zumunta to saidai wani bincike ya tabbatar da wannan magana ta Kanu.
Binciken wanda jaridar Premiumtimes ya gudanar ta gano cewa, garin Jada wanda Atikun ya fito a ciki yana karamar hukumar Ganye ne dake jihar Adamawa, wanda nanne asalin kabilar Chamba.
Wannan yanki asali yana cikin kasar Kamarune wanda sai a shekarar 1961 ne aka gudanar musu da zabe suka kuma zabi su hade da Najeriya.
Saidai a lokacin da aka haifi Atiku a shekarar 1946, yankin Jada yana cikin kasar Kamarune, bangaren turawan mulkin mallaka na Ingila, amma daga baya aka hade su suka zama Najeriya.
Saidai abin lura shine a hukumance Atiku dan Najeriya ne saboda yankin Jada yana cikin Najeriya

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Asalin Atiku Abubakar dan kasar kamaru ne"

Post a Comment