Haramcin Kudin Internet Bitcoin - Fatawa

Babban malamin addinin musulunci na kasar Masar, Shawki Ibrahim Abdel-Karim Allam, ya fitar da wata fatawa inda ya haramta amfani da kudin intanet na Bitcoin.
A fatawar da a ka wallafa ranar Litinin, Shawki Allam ya ce ba a yarda musulmai su siya ko su siyar ko kuma su biya haya da wannan tsari na Bitcoin ba.
Ya ce amfani da kudin intanet na da hadari domin zai iya haifar da zamba da yaudara, kuma kasancewar tsarin maras tabbas, ya na iya cutar da jama'a da ma kasashe.
Babban malamin ya ce sai da ya nemi taimakon masana tattalin arziki kafin ya yanke wannan hukunci.
Mene ne Bitcoin?
Bitcoin na da abubuwa biyu da suka bambanta shi: kudin intanet ne kuma ana ganinsa a matsayin wani abu da za a iya amfani da shi a madadin kudi.
kan intanet sabanin kudaden takarda ko sulalla da ke aljihunka
Duk da cewa akwai wasu na'urorin bayar da kudi (ATM) na musamman da ke bayar da Bitcoin, ya fi dacewa a yi tunaninsu kamar 'yan kudaden intanet.
Kuma babu gwamnati ko kuma bankin da ke buga Bitcoin.
Wannan na nufin "ba kudin da doka ta amince da shi ba ne, ba za ka iya biyan harajinka ko kuma ka yi amfani da shi wajen biyan bashi ba", in ji Dr Garrick Hileman na fannin koyar da kasuwanci a jami'ar Cambridge.
Ana samar da Bitcoins ne ta wata hanya mai sarkakiya da ake ce wa "haka" (wato "mining, a Ingilishi), sannan wasu komfuntoci da ke hade a fadin duniya za su saka ido kansa.
Ana samar da kimanin Bitcoin 3,600 a ko wace rana - kuma a halin yanzu akwai kimanin kudin miliyan 16.5 da ke yawo.
Sai dai kuma, kamar dukkan kudade, darajarsa ya dangata ne ga iya kudin da mutane suke son saye shi tare da sayar da shi.

bbchausa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Haramcin Kudin Internet Bitcoin - Fatawa"

Post a Comment