Fanfanfan: Buhari ya lashe zabukan jihohi mafi yawan kuri'u, watau Kano da Legas

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya lashe zaben jiha ta biyu mafi yawan masu kada kuri'u, watau Kano inda ya baiwa dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ratar kuri'u sama da miliyan daya.
Sakamakon da INEC ta bayyana ya nuna cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu kuri'u 1,464,768, yayinda Atiku Abubakar kuma ya samu kuri'u 391,573.

Dama dai tuni Buharin ya lashe zaben Legas, jiha ta daya mafi yawan masu zabe a Najeriya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Fanfanfan: Buhari ya lashe zabukan jihohi mafi yawan kuri'u, watau Kano da Legas"

Post a Comment