PDP ta yi watsi da sakamakon zaben da INEC ke sanara

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta sanar da cewa ba za ta iya kau da kai ga abin da ta kira hatsarin da demokradiyyar Najeriya ke daf da fada wa ba.
A wata sanarwa da shugaban jam'iyyar Prince Uche Secondus ya fitar, jam'iyyar ta ce sakamakon da ke hannunta daga jami'anta da ta tura sassan kasar sun ci karo da wanda hukumar zabe ta INEC, kuma ta ce ba ta amince da su ba.
Jam'iyyar ta kuma zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyarsa ta APC da hada baki da hukumar zabe ta kasa, INEC kamar yadda ta ce domin su karkatar da akalar siyasar kasar.
Ta yi kira ga 'yan Najeriya su yi watsi da sakamakon zabukan da kawo yanzu hukumar zaben ta bayyana.
Jam'iyyarta PDP ta kuma zargi jam'iyyar APC da murde zabukan da aka yi ta hanyar bayar da cin hanci ga masu zabe, da kuma tursasa wa mutane su zabe ta.
Ta kuma ce APC ta yi amfani da jami'an tsaro na 'yan sanda da sojojin Najeriya har ma da jami'an tsaro na cikin gida DSS har da hukumar EFCC domin razana abokan adawarta.
Sannan jam'iyyar ta PDP ta zargi APC da kokarin dakile sakamakon zaben, kamar yadda ta ce, APC ta tura wasu manyan jami'an gwamntinta su karkatar da sakamakon.
A karshe jam'iyyar ta PDP ta ce kama Injiniya Buba Galadima da ta ce gwamnatin Buhari ta yi ya nuna karara cewa Buhari ya kafe sai ya ci gaba da mulki ko da jama'ar kasar sun zabi wani jagoran na daban.
Ta kuma yi kira da da a sake shi ba tare da bata lokaci ba.
Chief Uche Secondus ya tabbatar wa mabiya jam'iyyar cewa tana kan hanyar samun cikakken nasara a wannan zaben.
Ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su sa baki a cikin abin da ta kira kwacen da jam'iyyar APC ke son yi mata domin kwato kasar daga matsalolin da ke jiran 'yan kasar idan ba a dauki mataki ba.
Source: BBChausa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "PDP ta yi watsi da sakamakon zaben da INEC ke sanara"

Post a Comment