GANDUJE: GWAMNA UKU A CIKIN GUDA

GANDUJE GANDUN AIKI. Shine inkiyarsa a jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kafa tarihin mataimakin gwamna kadai a fadin jihar Kano da ya yi zangon wa’adin mulki har karo biyu. Ganduje ya sake kafa tarihi a siyasar jihar Kano a matsayinsa na mataimakin gwamna da ba a taba jin kan su da Gwamna yayin da suke mulki, sabanin sauran gwamnonin da ba su wanye lafiya da mataimakansu ba. Kana kuma ya na da tarihin shine kadai mataimakin gwamna a jihar da ya ke da gidauniyar tallafawa al’umma mai suna Ganduje Foundation.
An yabe shi a matsayin mai matukar hakuri da juriya gami da iya kyautata mu’amala da mutane. Ganduje ya zama Gwamna na farko a tarihin siyasar jihar da wani Gwamna mai ci ya riko hannun sa kana kuma ya yi sa’ar zama Gwamna.
Shan alwashin kammala ayyukan da ya gada a wajen Kwankwaso da kuma wanda Shekarau ya fara bai kammala ba, wannan babban abin yabawa ne. Wanda Hakan ya mayar da shi Gwamna na farko a tarihin jihar Kkano da ya kammala ayyukan Gwamnonin da ya gada. Biyan ma’aikata albashi akan kari sabanin wasu gwaamnoni da ake kuka da su, tare da yi wa malaman makarantar firamare karin albashi da suka dade suna jira wannan abubuwa ne da suka janyo masa yabo.
Aikin gagarumar gadar karkashin kasa da ya ke yi a unguwar Kurna abin alfahari ne ga Kanawa musamman kasancewar titi ne mai matukar cunkoso da ya dade yana addabar al’umma. Malala kwalta a wasu tituna da yi wa titin gidan gwamnati kwaliiya ya kara fito da jihar Kano.
Ganduje yana da kokarin ziyarar ta’aziyya gami da saukin kai, kamar yadda ya zama Gwamna na farko a jihar Kano da ya mallaki matakin karatun Dakta daga makaranta ba na girmamawa ba. Ganduje ne Gwamna na farko a jihar Kano da ya yi Kantoma a kananan hukumomi biyu. Ganduje ya zama shine Gwmna na farko a jihar Kano da ya rike mukamin Kwamishina, tun a zamanin soja. Ganduje ya zama Gwamnan farko a jihar Kano mafi dadewa yana aikin gwamnati.
Idan ya zama Gwamna a karo na biyu, Ganduje zai zama Gwamna na uku da suka mulki jihar Kkano tsawon shekaru takwas, bayan Kwankwaso da Shekarau. Sannan zai zama Gwamna na biyu da ya maimaita mulkar jihar a jere bayan Shekarau.

Source: Maje El-Hajeej Hotoro.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "GANDUJE: GWAMNA UKU A CIKIN GUDA"

Post a Comment