Masu kutse sun katse intanet a Liberia

A lokuta da dama masu kutse sun yi ta katse
hanyoyin samun intanet a Liberia inda suka rufe
hanya daya tilo da kasar ke samun intanet din.
Hare-haren da suka rika kai wa wayar da ke
samar da intanet din ga kasar a ranar uku ga
watan Nuwamba sun sa intanet din ta rika
katsewa.
Masu bincike sun ce hare-haren sun nuna cewa
masu kutsen sun rika kokarin yin amfani da
hanyoyi da dama na satar bayanai daga wuraren
sirri.
Masana sun ce gungun masu kutsen ne ya taba
yin kutsen da taba durkusar da hanyoyion intanet
a kasar ranar 21 ga watan Oktoba.
Hare-haren na daha cikin manya-manyan kutsen
da suka hana samun intanet din manyan
shafukan intanet irin su Twitter, Spotify da kuma
Reddit.
Hare-haren na cikin wadanda aka fi yin amfani
da su wajen yada kwayoyin cutukan kwamputa
ga na'urorin da ba su da kariya sosai.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Masu kutse sun katse intanet a Liberia"

Post a Comment