Jami'an tsaro sun janye Trump daga wajen yakin neman zabe

An janye dan takarar shugabancin Amurka
Donald Trump daga kan dandamalin da yake
jawabi yayin yakin neman zabensa a jihar
Nevada sakamakon wani firgici da aka samu a
wajen.
Jami'an tsaro ne dai suka yi gaba da shi bayan
da wani ya yi kururuwa cewa ya ga wani da
bindiga a wajen; kodayake da aka bincika ba a
ga kowane irin makami ba.
An dai samu rudu tsakanin magoya bayan dan
takarar na jam'iyyar Refablika inda har wasu
suka nemi wurin gudu saboda kururuwar ta cewa
an shigo da bindiga a zauren.
Rudun ya karu lokacin da sojoji suka shigo
zauren amma da aka bincika ba a samu kowane
irin makami sai aka yi awon gaba da wani
mutum wanda ake zargin shi ne ya yi fara yin
kururuwar.
Bayan 'yan mintuna Mr. Trump ya dawo zauren
idan ya ci gaba da jawabinsa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jami'an tsaro sun janye Trump daga wajen yakin neman zabe"

Post a Comment