Manyan Jarumai Mata Guda 10 Da Tauraruwar Su Take Haskawa A Masana’antar Kannywood Daga Shekarar 2016 Zuwa 2017

Kamar yadda muka fada a baya, wannan zubin jadawali ya yi nazari ne na musamman ta hanyar duba da rawar da kowace jarumi ya taka a finafinan da suka fito a 2016, ya’alla bangaren fada, jarumta, barkwanci da sauran fannoni.
1- Hadiza Aliyu (Gabon) :
Fim din BASAJA GIDAN YARI kadai ya isa dora shahararriyar harumar a matakin na farko. Ba tantama wannan jaruma ta nuna kanta a cikin shirin. Babu wani abu da za a iya cewa game da ita sai sambarka. Hakika babbar nasara ce a wajen jarumar da ta zamo cikin jerin wadanda suka taka rawa a cikin fim din Basaja. Ta shiga tarihin da ba za a manta da ita ba, domin kusan kowa ya fi ganin ta fiye da sauran jaruman.
Yanayin yadda Zee take wasa kwakwalwarta a duk lokacin da take kokarin gano halin da Jabir yake ciki akwai mamaki matuka. Domin idonta, bakinta, kunnenta da duk ilahirin jikinta yana nunawa dan kallo cewar lallai abinda take fada haka yake. Hadiza Gabon ba daga nan ba, hakika ta ciri tutar da za ta iya lashe kowace irin kyauta ta girmamawa.
Jarumar haifaffiyar kasar Gabon, ta shigo masana’antar finafinai da kafar dama, domin kuwa ta samu nasarar bankwarawa tare hawa bigiren da dukkan wani shahararre yake buri.
Sai dai ba wai daukakar da Allah ya yi wa jarumar ko kuma kwarewa da ta yi a harkar fim bane ya fi ja hankalin mutane ba, sai don wasu kyawawan dabi’u da Allah ya azurta jarumar da su, wadanda da yawan al’umma ba su da su, ba ma kawai abokan sana’arta na fim ba. Domin Hadiza ta kasance mai tausayi da jin kan al’umma domin abin hannunta bai dame ta ba.
Ta taba fadin: “Na samu nasarori da kyaututtuka da dama, ciki har da kyautar tauraruwar taurari mata da kuma kyautar da gwamnan Kano ya bani har ma kuma da kyautar da na samu a da fim din Ali ya ga Ali,” in ji Hadiza Gabon.
Fitacciyar jarumar ta lashe kyautar ‘yar wasan da ta fi tallafawa babban jarumi a fim, a wani bikin bayar da kyaututuka ta Africa Films Awards na shekarar 2016 wanda jaridar Africa Boice take gudanarwa a kasar Ingila.
2- Hafsat Idris :
A rana irin ta yau, watau 16 ga watan Dismabar 2015, jarumar ta fara daukar kyamara a farfajiyar shirya finafinan Hausa, inda ta fito a cikin fim din BARAUNIYA . Duk da cewa shi ne fim din na farko, amma tun kafin ya fita kasuwa jarumar ta fara samun yabo daga masana harkokin finafinan Hausa.
Cikin shekara daya kacal da fara yin fim, jarumar ta zamo tauraruwar da kowane lungu da sakon ake labarinta. Gwana ce wajen iya aktin, musamman da ta kasance tana iya taka kowace irin rawa da aka dora ta.
Da farko an yi tsammanin Hafsat Idris za ta rika fitowa ne a matar aure kawai, amma daga bisani sai kwarewarta ta fito fili ta yadda take iya fitowa a finafinai kala-kala.
Masana’antar Kannywood ta dade ba ta samu jaruma da cikin lokacin kankani ta shige sahun takwarorinta ba, domin an saba ganin yadda wasu jaruman ke daukar shekaru kafin ‘yan kallo su gamsu cewar kwararru ne.
Babban abin da ya fi jan hankalin makallata finafinan Hausa game da jarumar shi ne, irin salon kifta idonta a lokacin da take magana. Wasu na ganin jarumar ta fito da nata irin salon ne domin ta kwashi magoya baya, wanda yanzu haka take samunsu a kullu yaumin.
Finafinan da suka sanya jarumar ta haye sahu na biyu a wannan jadawali sun hada da; Furuci, Dan Kurma, Maya, ‘Yar Fim, Wazeer da sauran su.
3- Rahma Sadau :
Duk ba dakalar korar jarumar da ta kunno kai a karshen shekarar nan, hakan bai hana Rahma samun kanta a jerin jarumai mata da suka haska a 2016 ba, domin za a iya cewa jarumar ta samu nasarar tsallake Arewacin kasar zuwa Kudancin Nijeriya, Afrika da ma kasashen duniya.
Ta wata fuskar, za a iya cewa korar Rahma daga masana’antar Kannywood gobar titi ce a Jos, domin yanzu ba jarumar Hausa ba ce, tuni ta fara mafarkin fitowa a finafinan industirin da babu kamarta watau Hollywood.
Tun kusan farkon shekarar nan, jarumar ta fara fuskantar kalubale daga masu ruwa da tsaki a farfajiyar Kannywood, sakamakon wani fim da ta fito a ciki mai suna ANA WATA GA WATA , inda ta yi wani kalami da ake ganin bai dace ba, an so dakatar da fitar fim din, amma daga bisani aka sake shi kasuwa, duk da an samu matsaloli da dama da suka hada da kame jigajigan da suka hadu wajen samar da shirin.
Rawar da jaruma Rahma Sadau ta taka a fim din Ana Wata Ga Wata ta fita daban, domin ta janyo mata suna da shahara a fadin Nijeriya.
Bullar labarin korar ta kuwa, shi ne labari na farko na wani jarumin Kannywood da ya zagaya duniya.
Jim kadan bayan balahirar, Rahma ta samu gayyata daga shahararren mawaki Akon zuwa kasar Amurka, inda ta shafe tsawon kwana 10 tana warkajami a tsakiyar turawa.
Hakika shekarar 2016 ta zowa jarumar da abu biyu; farko kalubalen kora daga abokan aikinta na asali watau Kannywood, da kuma nasarar samun gayyata zuwa Hollywood. Yanzu haka akwai fim dinta na Turanci mai suna SONS OF THE CALIPHATE da ake haskawa a gidan talabijin na Ebony Libe.
4- Nafisa Abdullahi :
GUGUWAR SO, fim ne da ya yi masifar kyau, musamman da ya kasance labarin soyayya. Hakika jarumar ta tuna da irin rawar da ta taka a fim din da ya zama silar zamowarta shahararriya a duniya finafinai watau, Sai Wata Rana.
Jarumar ta haskaka sosai a wannan shekara, sunan ta bai boyu ba sam, musamman bayan ta kaddamar da gidauniyar tallafawa gajiyyayu kwanan baya.
Nafisa jaruma ce da ta kware wajen iya salon aktin na soyayya ko kuma salihanci. Tana yin kyau kwarai idan ta fito a matsayin wadda ake zalunta. A shekarar nan ta fito a shirin fim mai dogon zango wanda Darakta Malam Aminu Saira ya bada umarni, watau LABARINA. Tallar shirin kawai aka gani, amma tuni mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu game da rawar da Nafisa ta taka.
Game da gidauniyar da ta bude kuwa, Nafisa ta ce dalilin da ya sa ta kaddamar da wannan Gidauniya ta kuma fara da taimakon talakawa shi ne, bisa rahoto da ta samu na irin matsaloli da al’umma ke fuskanta musamman na rashin dan abin da za a kai bakin salati. A cewarta, lokaci ya yi da ya kamata mutane irinsu su fara taimakawa jama’a ta hanyoyin da suke ganin za su iya.
“A duk lokacin da mutum ya kai matsayin da jama’a suke kaunarsa, musamman dan fim da yake alfahari da jama’a, kasancewar su ne ke siyan finafinan da yake fitowa a ciki. Ya dace ya dauki matakin bin hanyoyin da zai tallafa masu, ko ya samu lada a wajen ubangiji.” In ji Nafisa.

Download video now

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Manyan Jarumai Mata Guda 10 Da Tauraruwar Su Take Haskawa A Masana’antar Kannywood Daga Shekarar 2016 Zuwa 2017"

Post a Comment