*_NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI_*
*FITOWA TA 1*
(Masoyinki ya rabauta, mai zagin ki ya yi hasara)
Dukkan yabo, godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su qara tabbata ga Manzon Rahama, tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi, Sahabbansa da Iyalansa Iyayen Muminai bisa nassin al-Qur’ani.
‘Yan uwa, sananniyar Magana ce cewa inda za a taskace dukkan takardu da alqaluma ba za su iya rubuce daraja da matsayin uwar Muminai Nana Aisha, Allah ya qara yarda a gare ta ba, sai dai zuciyata, ta nutsu akan in rubuta ‘yar taqaitacciyar saqo, wanda zai qara taimakawa qananan dalibai irina wajen qara fito mana da wasu daga cikin abubuwan da ya kamata mu sani game da ita.
1. WACE CE NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA???
Ita ce uwar Muminai Ummu Abdullahi. Aisha diyar Shugaba kuma mai gaskiya, Khalifan Manzon Allah, tsaira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi, wato Abubakar wanda shi ne Abdullahi dan Abi Quhafah, Uthman dan Aamir dan Amru dan Ka’ab dan Lu’ayyin Baquraishiya, Uwar Muminai, Iyalin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda Malamai sun sallama cewa ita ce ma fi sanin addini a cikin Matan Duniya bakidaya.
Mahaifiyarta kuwa, ita ce: Ummu Ruuman diyar Aamir dan Uwaimir dan Abdu Shams dan Itaab.
Iyayenta sun yi hijira tare da ita kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya aure ta kafin ya yi hijira bayan rasuwar Nana Khadijah diyar Khuwailid, Allah ya qara yarda a gare ta, da watanni goma da ‘yan kwmanaki, wasu malamai kuma suka ce da shekara biyu sannan ya tare da ita a watan Shawwal shekara ta biyu bayan dawowansa daga yaqin Badar a lokacin tana da shekaru tara (9) da haihuwa, don haka ta ruwaito ilimi mai tarin yawa kuma masu albarka daga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Yada wannan sako a matsayin naka gudunmuwar na nuna kauna a gare ta.
A saurari fitowa na biyu in sha Allahu
✍ Dan uwanku A Musulunci
*Umar Shehu Zaria*

0 Response to "*_NANA AISHA, ALLAH YA QARA YARDA A GARE TA, UWA CE GARE NI_*"
Post a Comment