Shugaba Jacob Zuma na fuskantar sabon zargin rashawa

Wani bincike da aka gudanar kan zargin cewa
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu yana
huldar da ba ta dace ba da wasu hamshakan 'yan
kasuwa, ya ce ya gano wata shedar
almundahana kan shugaban.
Rahoton wanda aka dade ana jiran fitowarsa ya
bukaci Shugaba Zuman ya kafa kwamitin bincike
na shari'a cikin kwana 30, kan abubuwan da aka
gano.
Tun da farko Shugaban ya janye wata kara da ya
shigar, wadda yake neman hana ko jinkirta fitar
da rahoton, wanda wani bangarensa ya binciki
alakarsa da hamshakan attajiran 'yan kasuwar
nan da ake kira iyalan Gupta.
Rahoton mai shafi 355 ya bukaci da a kara
bincike a kan zargin almundahana, da ya hada da
sayen wani wurin hakar ma'adanai da kamfanin
Teget, wanda dan Shugaban, Duduzane Zuma, ya
mallaki wani bangarensa ya yi.
'Yan sanda sun yi amfani da gurneti-gurneti na
roba domin tarwatsa masu zanga-zanga da ke
neman Shugaban ya sauka daga mulki.
Sama da shekara goma Shugaban kuma jagoran
jam'iyyar ANC, yake fama da zargin cin hanci da
rashawa, abin da a kullum yake musantawa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Shugaba Jacob Zuma na fuskantar sabon zargin rashawa"

Post a Comment