INEC: Ana zanga-zanga a Garin Abuja

Ana zanga-zanga a Birnin Abuja yanzu
haka saboda zaben Jihar Ribas
– A yau Talata, 8 ga wata masu zanga-
zanga suka burma Birnin-Tarayya Garin
Abuja
– Ana zargi Hukumar zabe za ta bada
sakamakon bogi a zaben Jihar Ribas
Ana zanga-zanga a garin Abuja yanzu haka
dalilin zaben Jihar Ribas.
Jaridar Premium
Times ta rahoto cewa masu zanga-zanga
sun dura Birnin Tarayya harin Abuja da
zargin Hukumar zabe ta INEC za ta fitar da
sakamakon bogi a zaben Jihar Ribas da za a
gudanar kwanan nan.
Ana ta yada cewa Hukumar zabe ta INEC za
ta fitar da sakamakon karya na jabu a zaben
Ribas da za a karasa kwanan nan. Ana cewa
Kwamishinar zabe ta INEC, Aisha Zakari tana
kokarin hada kai da ‘Yan siyasar APC masu
mulki wajen yin magude a zaben da za a
gudanar.
Ana dai zargin Aisha Zakari da yunkurin hada
kai da ‘Yan siyasar Kasar na Jam’iyyar APC
mai mulki wajen fitar da takardun zabe na
jabu, sai dai babu wata hujja da ke gaskata
wannan zargin na su. Masu zanga-zanga
suna kira da a tsige Kwamishinar Hukumar
zaben watau Aisha Zakari.
A makon jiya ne dai Hukumar zabe ta Kasa
watau INEC ta sa ranar 10 ga watan
Disamba a matsayin ranar da za a karasa
ragowar zaben ‘Yan Majalisun da suka rage a
Jihar Ribas. An ta kokarin gudanar da zaben
a baya, sai dai ko yaushe, sai da rigima ake
karewa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "INEC: Ana zanga-zanga a Garin Abuja"

Post a Comment