An gano riga-kafin karya lagon sauro

Wani riga-kafin zazzabin cizon sauro ya samu
gagarumar nasara a gwajin da aka yi wa Dan
adam.
Likitoci sun yi amfani da wani nau'in sauro da
aka jirkita kwayar halittarsa ta yadda ba ya
harbin mutane da cutar.
Gwaje-gwajen wadanda aka wallafa a mujallar
Science Translational Medicine sun nuna cewa
riga-kafin na da aminci kuma yana bai wa jiki
kyakkyawar garkuwa.
Kwararru kan sha'anin cutukan da ake samu a
kasashe masu zafi sun bayyana binciken a
matsayin "abin amfani,
Jami'ai a cibiyar bincike kan cutuka masu
yaduwa a Seattle sun cire wasu kwayayen halittu
guda uku a jikin sauro ta yadda ba zai iya harbin
kwayoyin halittar hanta da cuta ba.
Mutum goma aka yi wa gwajin don tabbatar da
amincin riga-kafin, a cikinsu ba wanda ya kamu
da zazzabi kuma maganin ba shi da wata
matsananciyar illa.
Wani kwararre, Sir Brian Greenwood na cibiyar
tsafta da magungunan kasashe masu zafi ta
London ya ce abin yana da karfafa gwiwa, amma
shi matakin farko ne na samun wata allurar riga-
kafi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An gano riga-kafin karya lagon sauro"

Post a Comment