Gambia: Minista ya yi murabus domin kyamar Jammeh

Ministan sadarwa na kasar Gambia, Sheriff
Bojang, ya sanar da yin murabus daga kujerarsa,
a wani mataki na matsa wa Yahya Jammeh
lamba da ya sauka daga shugabancin kasar.
Mista Bojang ya ce ya yi hakan ne domin nuna
kin amincewa da yunkurin shugaba Yahya
Jammeh, na karya dimokradiyyar Gambia.
Sheriff Bojang wanda ya shaida wa kamfanin
dillanci labarai na Reauters hakan, ya kuma ya yi
kira ga sauran masu rike da mukamai irin nasa
da su ma su kwata irin abin da ya yi.
Gidan talbijin mallakar kasar dai ya bayyana
cewa shugaba Jammeh ya yi wa mista Bojang
Korar kare daga aiki ba murabus ya yi ba.
A yau ne dai ake sa ran kotin kolin kasar za ta
fara sauraron karar da shugaba Yahya Jammeh
ya shigar yana kalubalantar sakamakon zaben da
ya ba wa abokin adawarsa, Adama Barrow
nasara, a kansa.
Amma kuma rahotanni na cewa har yanzu
alkalan kotun wadanda ake zargin an yi hayarsu
daga Najeria da Sierra Leone, ba su kai ga isa
Gambiyar ba.
A ranar Litinin ne dai shugabannin wasu kasashe
a Afirka ta Yamma suka yi wani taro a Abuja,
babban birnin Najeriya, kan makomar siyasar
Gambia.
Sun kuma yanke shawarar sake komawa kasar
domin lallashin shugaba Jammeh ya mika mulki
ranar 19 ga watan Janairun nan.
Shugaban Gambia mai ci, Yahya Jammeh dai ya
sauya aniyarsa ta kin amincewa da shan kaye,
kasa da mako daya bayan ya amince da faduwa.
Jammeh ya nemi da a sake zabe, a inda kuma
sojoji suka karbe ragamar iko da hukumar zaben
kasar, bayan da shugaban ya zarge ta da tafka
masa magudi.
yi amai ya lashe
Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben Gambia
Wasu dai na danganta kin amincewa da shan
kayen da Jammeh ya yi da kalaman da
zabbabben shugaba, Adama Barrow ya rinkayi
cewa za su bi doka wajen gurfanar da Yahya
Jammeh.
Kusan za a iya cewa yanzu haka kallo ya koma
kasar Gambia domin sanin abin da zai je ya zo
daga ranar 19 ga Janairu, ranar da ya kamata
Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Gambia: Minista ya yi murabus domin kyamar Jammeh"

Post a Comment