Nigeria: Tsohuwar ministar mai ta mika dala miliyan 153 ga EFCC

Tsohuwar Ministar albarkatun mai ta Nigeria
Diezani Alison-Madueke ta mika wa gwamnatin
kasar dalar Amurka miliyan 153 da ake zargin ta
sata daga asusun gwamnati.
Hakan dai ya biyo bayan wani hukunci da wata
kotu ta yanke a birnin Legas ranar Jumu'a cewa
matar ta mika wadannan kudaden ga gwamnatin
har a tabbatar da halaccinsu ko akasin haka.
A cewar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin
kasar zagon kasa ta EFCC - wadda ita ce ta
bukaci kotun da ta umarci tsohuwar ministar ta
mika kudin - an sace kudin ne daga kamfanin mai
na NNPC kana aka boye su a wasu bankuna uku
da ke kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar NAN ya ce
Alkalin kotun Muslim Hassan wanda ya ba da
wannan umarnin; ya bai wa jami'an bankunan
uku wa'adin kwanakki 14 su bayyana gabansa
domin su kawo masa shaidar da ke nuna cewa
kudin ba na sata ba ne.
Ya ce idan suka kasa yin hakan to za a sallama
kudin kacokan ga gwamnatin tarayyar Najeriya.
'Yadda aka saci kudin'
A cikin bukatar neman mika kudaden wadda
jami'in bincike na hukumar ta EFCC Moses
Awolusi ya gabatar wa kotun, hukumar ta ce a
watan Disamba na shekara ta 2014 ne tsohuwar
ministar ta kira babban manajan daya daga cikin
bankunan a ofishinta suka tsara yadda za a saci
kudaden.
Jami'in hukumar ya yi zargin cewa Mrs Diezani
Alison-Madueke ta bukaci babban manajan
bankin da ya tabbatar da cewa ba a saka kudin a
cikin asusun da aka san da zamansa ba kuma ba
a rubuta shigar da kudin ba cikin kundin da
bankin ke rubuta huldodin da ya yi ba.
Rahoton na kamfanin dillancin labaran Najeriyar
dai bai fadi ko lauyoyin tsohuwar ministar suna a
kotun lokacin wannan zaman ba; balle martanin
da suka mayar ga wadannan zarge-zargen.
Amma dai wannan ba shi ne karon farko da ake
zargin ministar da almundahana ko facaka da
kudaden jama'a ba, amma kuma a kodayaushe
takan musanta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Tsohuwar ministar mai ta mika dala miliyan 153 ga EFCC"

Post a Comment