An hana sojin Nigeria shiga shafukan sada zumunta

An hana sojojin Najeriya wallafa hotuna ko
bidiyon ayyukansu a shafukan sada zumunta.
Wannan mataki ya biyo bayan fitar wani faifan
bidiyo ne a kwanakin baya, inda aka nuna wasu
sojoji suna korafin karancin abinci da sauran
kayan aiki.
Sojojin dai na cikin wata runduna ne da ke yakar
kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabashin
kasar.
A wani jawabi da ya gabatar a madadin
Shugaban rundunar sojin kasar Tukur Buratai a
birnin Kaduna, Manjo-Janar Adeniyi Oyebade ya
yi kira ga sojojin da su yi taka-tsan-tsan.
"Ina gargadin ku kan amfani da shafukan sada
zumunta a lokacin da kuke cikin aiki.
Za ku iya jin kuna bukatar daukar hotunan
abokan aikinku masu kyau, amma ku yi taka-
tsan-tsan wurin yin hakan," in ji shi.
Ya kara da cewa "ku kau cewa wallafa duk wani
hoto ko bidiyo wanda ya shafi abokan aikinku ko
kuma aikin naku kai tsaye".
Ana yawan yada hotuna da bidiyon dakarun
Najeriya musamman wadanda ke fagen dagar
yaki da Boko Haram.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An hana sojin Nigeria shiga shafukan sada zumunta"

Post a Comment