'Yadda fyaɗe ke ƙara ta'azzara a arewacin Najeriya'

Wata kungiya mai zaman kanta da ke ayyukan
kula da mata da kananan yara da marayu a jihar
Kadunan Najeriya, mai suna ARRADA, ta ce,
fyade na karuwa yadda ba a zato, a arewacin
Najeriya.
Hajiya Rabia Ibrahim, shugabar kungiyar ta
ARRADA, ta bayyana wa BBC cewa, an sami
batutuwan yi wa yara maza da mata fyade fiye
da 100 a shekarar 2016.
Sai dai kuma ta ce batutuwan da suka fi zafi da
daukar hankalin mutane sun fi guda 50 wadanda
aka samu a daga watan Agusta zuwa Disambar
2016.
Hajiya Rabia ta zayyana manyan fyaden da aka
samu kamar haka
A Kaduna, wani dagaci mai shekara fiye da
80, ya karbi wata yarinya da ta bata kuma da
shi da dansa da jikansa duka sun kwashe
shekara guda suna yi wa yarinyar fyade.
Yaro dan shekara biyar ya gamu da ajalinsa,
bayan da wani matashi mai shekara 12 ya yi
lalata da shi, a Zariya.
Wata yarin 'yar shekara hudu ta samu
matsalar kasa rike bayan gida sakamakon
fyaden da aka yi mata ta gaba da bayanta.
An kuma sami wani magidancin da yake yi
wa 'ya'yan cikinsa guda uku fyade da suka
hada da mai shekara biyu da hudu da kuma
'yar wata bakwai wadda cikinta ya kumbura
saboda hadiye maniyyin mahaifin nata.
Hajiya Rabia ta kuma koka kan yadda ake samun
jan kafa tsakanin hukumomin 'yan sanda da
bangaren Shari'a wajen hukunta masu aikata irin
wannan laifi.
Ta kara da cewa rashin hukunta wadanda aka
samu da laifin ne yake sanya al'amarin yake kara
ta'azzara.
To amma shugabar kungiyar ta ARRADA, ta
shawarci jama'a musamman iyaye kan yadda ya
kamata su kula da kai komon 'ya'yansu.
Ya kamata iyaye musamman mata su sanya
ido kan masu kula da 'ya'yansu, misali direba
ko kuma mai aiki.
Iyaye su kula sosai da mutanen da 'ya'yan
nasu suke matukar shakuwa da su misali
ankul ko anti da dai sauransu.
Kula da masu yawan yi wa yara wasa ko
kuma ba su kyaututtuka.
Ka da iyaye su rinka korar 'ya'yansu da su je
su yi wasa domin kyale su shakata.
Iyaye mata su rinka duba al'aurar 'ya'yansu
musamman idan suka zo suna kuka tunda
dai ba sa iya magana.
Sharhi, Usman Minjibir
Kusan dai za a iya cewa matsalar fyade a
arewacin Najeriya na daya daga cikin wasu
matsaloli da ake samu amma kuma ba a son
daga maganar.
Masana suna alakanta rashin bunta zancen
fyade ga dalilai na addini da al'ada da kuma
rashin son kunyata a cikin al'umma.
Sau da yawa a kan samu iyaye maza da suke yi
wa 'ya'yansu 'yan mata fyade amma saboda
gudun abin kunya, a kan lullube maganar.
A mafi yawancin lokaci, da zarar an daga irin
wannan maganar, abin da ke biyo baya shi ne
kyama daga wurin al'umma.
A kan samu yanayin ma da yarinya ba za ta
samu manemi ba sakamakon fuskantar matsalar
fyade duk kuwa da cewa ba a son ranta aka yi
mata fyaden ba.
Ana dai ganin cewa da za a rinka kai maganar ga
mahukunta kuma ba tare da wata-wata ba a
hukunta duk wanda aka samu da laifi, to da
al'amarin ya bai kai haka ba.
Arewacin Najeriya dai na daya daga cikin
yankuna masu dimbin al'umma musulmai a
nahiyar Afirka.
Kuma yankin ne yake gaba a yawan musulmai a
Najeriya.
Har ma wasu jihohin yankin na ikrarin kwatanta
zartar da Shari'a bisa doran AlQur'ani.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Yadda fyaɗe ke ƙara ta'azzara a arewacin Najeriya'"

Post a Comment