Riyad Mahrez na Algeria ne gwarzon Afirka na 2016

Dan wasan gaba na Algeria Riyad Mahrez shi ne
ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na
CAF na 2016.
Mahrez wanda ya ke yi wa Leicester City wasa a
gasar Premier ya taka muhimmiyar rawa a kofin
gasar Premier da kungiyar ta dauka a kakar da
ta wuce, inda ya ci musu kwallo 17.
A watan Disambar da ya gabata, Mahrez ya
samu kyautar gwarzon dan wasan Afirka na BBC
na 2016.
A bangaren mata kuwa, Asisat Oshoala 'yar
Najeriya ita ce ta zama gwarzuwar 'yar wasan
kwallon kafa ta Afirka ta 2016 ta CAF.
An gudanar da bikin raba kyautukan ne a Abuja
babban birnin tarayyar Najeriya.
A shekarar 2015 dai Pierre-Emerick Aubameyang
ne ya lashe kyautar ta CAF.
Kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta 2016
1. Riyad Mahrez (Algeria da Leicester City) -
Kuria 361
2. Pierre-Emerick Aubameyang (Gabon da
Borussia Dortmund) - Kuria 313
3. Sadio Mane (Senegal da Liverpool) - Kuria 186
votes
Gwarzon dan kwallon Afirka mai taka-leda a
Afirka
1. Denis Onyango (Uganda da Mamelodi
Sundowns) - Kuria 252
2. Khama Billiat (Zimbabwe da Mamelodi
Sundowns) - Kuria 228
3. Rainford Kalaba (Zambia da TP Mazembe) -
Kuria 206
Macen da ta fi kwazo a 2016
Asisat Oshola (Nigeria da kungiyar mata ta
Arsenal )
Matashin dan kwallo mai tashe
Kelechi Iheanacho (Nigeria da Manchester City)
Matashin dan wasan da ya taka rawa
Alex Iwobi (Nigeria da Arsenal)
Mai horor da tamaula da babu kamarsa
Pitso Mosimane (Mamelodi Sundowns)
Kungiyar tamaula da ta fi fice
Mamelodi Sundowns
Tawagar kwallon kafa da ta taka rawar gani
Uganda
Tawagar kwallon kafa ta mata da ta taka rawar
a 2016
Super Falcons ta Nigeria
Alkalin wasan kwallon kafa da babu kamarsa
Bakary Papa Gassama (Gambia)
Shugaban kwallon kafa da babu kamarsa
Manuel Lopes Nascimento, shugaban hukumar
kwallon kafa ta Guinea Bissau
'Yan mazan jiya a kwallon kafar Afirka
Laurent Pokou - Tsohon dan kwallon Cote
d'Ivoire, wanda ya mutu a watan Nuwambar 2016
Emilienne Mbango - Kamaru
Kyautar mai masaukin baki
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari
'Yan wasan Afirka 11
Mai tsaron bayar: Denis Onyango (Uganda da
Mamelodi Sundowns)
Masu tsaron baya: Serge Aurier (Cote d'Ivoire da
Paris Saint-Germain), Aymen Abdennour (Tunisia
da Valencia), Eric Bailly (Cote d'Ivoire da
Manchester United), Joyce Lomalisa (DR Congo
da AS Vita)
Masu buga tsakiya: Khama Billiat (Zimbabwe da
Mamelodi Sundowns), Rainford Kalaba (Zambia
da TP Mazembe), Keegan Dolly (South Africa da
Mamelodi Sundowns),
Masu cin kwallo: Pierre-Emerick Aubameyang
(Gabon da Borussia Dortmund), Sadio Mane
(Senegal da Liverpool), Riyad Mahrez (Algeria da
Leicester City)
Masu jiran kar-ta-kwana
Aymen Mathlouthi (Tunisia da Etoile du Sahel),
Kalidou Koulibaly (Senegal da Napoli), Salif
Coulibaly (Mali da TP Mazembe), Islam Slimani
(Algeria da Leicester City), Mohamed Salah
(Masar da Roma), Kelechi Iheanacho (Nigeria da
Manchester City), Alex Iwobi (Nigeria da Arsenal)

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Riyad Mahrez na Algeria ne gwarzon Afirka na 2016"

Post a Comment