Facebook Zai Fara Biyan Kudi Ga Masu Dora Hotunan Bidiyo

Barkanku da wannan lokaci na safiyar ranar alhamis. Kuna tare da Amanagurus ne a wannan lokaci da zan baku wani labari mai dadin ji musamman ga ma'abota dora videos akan kafar sadarwa zamani ta facebook.
Wasu daga cikin ku na sane da tsarin nan na youtube monetization wanda ake biyanka a duk video da ka dora akan youtube channel dinka sabili da wasu yan tallace-tallace da shafin youtube kan sanya a cikin hoton bidiyon.
Kamfanin facebook ma duba da irin yadda mutane ke karuwa kullum da kuma yadda yawan masu dora video ke karuwa yasa ya yanke shawarar kawo wannan tsari na video monetization don bawa masu amfani da kafar damar samun yan kudade da zasu amfani kansu.
Anyi ittifakin cewar a duk rana akan kalli bidiyo da yaka tsawon akalla awa miliyan dari a duk rana wanda hakan ne yasa kamfanin facebook yaga ya dace da ya fito da wannan tsari na monetization.
Ya zuwa yanzu dai wannan tsarin bai fara aiki ba, amma ana sa ran fitowar shi da zarar facebook sun gama tattauna yadda zasu tsara abubuwan.
Ina masu dora video akan facebook, yaufa ga dama ta samu, da zaku samu yan canji da zaku zuba a aljihunan ku....

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Facebook Zai Fara Biyan Kudi Ga Masu Dora Hotunan Bidiyo"

Post a Comment