Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama

– Bello Abubakar Masaba, mutumin da ya
auri mata barkatai ya riga mu gidan
gaskiya
– Bello Masaba ya mutu yana da mata
kusan 100
– Masaba yayi wasiyya da a rika aure
Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama
Idan ba a manta ba akwai wani ta’aliki
mai suna Bello Abubakar Masaba, a
Garin Bida ta Jihar Neja mai mata
barkatai. Wannan mutumi dai yanzu
Allah yayi masa cikawa a jiya Asabar
bayan yayi ‘yar gajerar rashin lafiya.
Masaba dai ya yanke jinki ya fadi har
sau biyu, daga karshen yace ga garin ku.
Wata Jarida mai suna The Eagle ta bada
labarin rasuwar wannan mutumi. Alhaji
Mutairu Salahuddeen; wani mai
magana a madadin wannna mutumi ya
tabbatar da haka.
Bello Masaba dai kowa ya san sa da
yawan mata, ace mai mata 97, yayi
mata kusan guda 107, ya kuma rasu ya
bar fiye da 80, bayan ya rabu da wasu
da dama. Ya haifi ‘ya ‘ya sama da 185,
sai dai wasu sun rasu, yanzu ya bar
akalla guda 133.
Bello Masaba dai ya rasu ne jiya da
rana, an kuma shirya jana’izar sa a
Ranar yau da safe. Marigayin yayi
wasiyya da a daina zinace-zinace a
koma auren mata na addini. Masaba ya
mutu yana da shekaru 93.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama"

Post a Comment