Buhari ya sake shan alwashin ceto 'yan matan Chibok

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce
yana fata nan ba da jimawa ba za a ceto sauran
'yan matan Chbok da aka sace kwana 1000 da
suka wuce.
Shugaba Buhari, wanda ya bayyana haka a
shafinsa na Twitter ranar Lahadi, ya kara da
cewa gwamnatinsa tana bakin kokarinta domin
ganin ta ceto 'yan matan da ma sauran mutanen
'yan Boko Haram suka sace.
A cewarsa, " Ina so na jaddada matsayina cewa
kamar yadda a baya na sha alwashin ceto su,
yanzu ma ba za mu karaya ba har sai mun
mayar da sauran 'yan matan hannun iyayensu".
Shugaban na Najeriya ya jinjina wa dakarun sojin
kasar bisa jajircewarsu wajen yaki da Boko
Haram, yana mai yaba wa dukkan mutanen da ke
fafutikar ganin an ceto 'yan matan.
An sake gano wata 'yar Chibok
Ziyarar 'yan matan Chibok ta bar baya da
kura
A ranar Lahadi ne ake cika kwanaki 1000 da
sace 'yan matan na makarantar Chibok 276 da
mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno da
ke arewa maso gabashin Nigeria.
Lamarin dai ya ja hankalin mutane da
gwamnatoci a sassan duniya daban-daban; inda
aka yi ta yin zanga-zangar neman a sako su.
'Sun cika kwana 1000 a tsare'
Fiye da 'yan mata 50 ne suka kubutar da kansu
tun ranar da aka sace sun wato 14 ga watan
Afrilun 2014, yayin da kawo yanzu gwamnati ta
samu kwato wasu kari 23.
A cikin wata sanarwa da ta fitar kan cika
kawanakki dubun da sace su, kungiyar kare
hakkin biladama ta Amnesty International ta yi
kira ga gwamnatin Najeriyar ta kara matsa kaimi
wajen ganin ta kubutar da sauran 'yan matan, da
ma wasu da ke hannun mayakan.Kungiyar ta
Amnesty ta kuma yi kira ga kungiyar Boko
Haram da ta kawo karshen ukubar da ta jefa
'yan matan dama sauran wadanda take rike da
su, don su koma cikin iyalansu.
Amnesty ta ci gaba da cewa, ba wai tana zargin
gwamnati da rashin kokari wajn kubuto da 'yan
matan da ma sauran wadanda aka sace ba ne,
tana so ne a kara himma saboda ba 'yan matan
kadai ne a hannun mayakan ba, har ma da wasu
mutane da suka hada da mata da yara.
Sai dai ta ce tana yaba wa gwamnatin kasar
kwarai da gaske wajen kubutar da sauran.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari ya sake shan alwashin ceto 'yan matan Chibok"

Post a Comment