Nigeria - An cire Ali Ndume daga shugaban masu rinjaye

Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da cire
Sanata Mohammed Ali Ndume a matsayin
shugaban masu rinjaye a majalisar. Inda ta
maye gurbinsa da Sanata Ahmed Lawal.
Shugaban majalisar, Bukola Saraki ne ya karanta
wasikar sauya shugaban masu rinjayen a zaman
majalisar a ranar Talata.
Jam'iyya mai mulkin kasar ta APC ce ta nemi a
sauya Ndume da Ahmed Lawal, a lokacin wani
taron 'ya 'yan jam'iyyar da ke majalisar.
Sanata Ahmed Lawal dai ya nemi zama
shugaban majalisar dattawan, amma bai yi
nasara ba.
Lamarin da ya raba kan 'yan jam'iyyar ta APC a
majalisar.
Sanata Ndume ya shaida wa BBC cewa ba a
tuntube shi a kan sauyin ba, kuma babu wanda
ya gayyace shi taron 'yayan jam'iyyar da ke
majalisar.
Babu wasu kwararan dalilai da aka bayyana na
sauyin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria - An cire Ali Ndume daga shugaban masu rinjaye"

Post a Comment