Kun taba ganin yarinyar da bishiya ke tsiro a jikinta?

Lokacin da wani tsiro mai kama da ɓawon
bishiya ya fara bayyana a fuskar wata yarinya
'yar shekara 10 Sahana Khatun wata huɗu da ya
wuce, mahaifinta bai damu ba.
Sai dai bayan sun fara yaɗo, ya damu matuƙa,
inda ya tafi kudu da ƙauyensu zuwa Dhaka
babban birnin Bangladesh don neman magani.
Yanzu likitoci na fargabar cewa Sahana ka iya
zama mace ta farko da ta taɓa fuskantar abin da
ake kira "larurar tsirowar bishiya a jiki".
Idan gwajin da suka yi ya tabbata, yarinyar ta
shiga rukunin wasu mutane 'yan ƙalilan a faɗin
duniya da ke fama da wannan larura mai suna
epidermodysplasia verruciformis.
Wasu mutane ƙalilan - duka maza ne- ake
tsammanin suna da wannan cuta.
Ga wasu mutanen, har ta ci ƙarfinsu, inda wani
mutum ba ma ya iya taɓa mata da ɗansa tsawon
shekara goma kenan.
Hannuwan Abul Bajandar duk wani tsiro ya fito
musu inda suka yi girman kilogram biyar, ga
kuma wani tofo a ƙafafuwansa, idan ka gan shi
tamkar bishiya.
Mutumin mai shekara 27, shi ne ɗan ƙasar
Bangaladesh na farko da aka gano na ɗauke da
cutar kuma a yanzu an yi masa aiki har sau 16 a
asibitin kwalejin koyon aikin likitanci ta Dhaka
don samun damar ci gaba da amfani da
hannunsa.
Likitoci na fatan cewa larurar Sahana ba irin
azababbiyar nan ba ce, don haka tana iya samun
sauƙi cikin hanzari.
Mahaifin Sahana, Mohammad Shahjahan ya ce
"Mu talakawa ne. 'Yata ta rasa mahaifiyarta tun
tana 'yar shekara shida. Ina da kyakkyawan fatan
cewa likitoci za su sassaƙe ɓawon bishiyar da ke
fitowa a kyakkyawar fuskar 'yata."

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kun taba ganin yarinyar da bishiya ke tsiro a jikinta?"

Post a Comment