MMM Nigeria Ya Dawo Aiki, Ko Menene Shi MMM Din?

Hadaddiyar cibiyar hada-hadar kudade ta MMM Nigeria ta fitar da sanarwar dawowa kan gudanar da harkokin kasuwanci gadan-gadan kamar yadda aka saba a can kwanakin baya.
Sanarwar dai ta fito ne ta shafin kafar na twitter a safiyar yau Juma'a inda suka bukaci jama'a dasu koma cikin harkar ba tare da wata fargaba ba duk da rade-radin da ake na cewar tsarin kasuwancin na iya kasancewa na yan damfara ne wanda ka iya rushewa da dukiyar mutane a kowanne lokaci.
A watan Disamban daya gabata ne dai kafar ta dakatar da duk wata hada-hadar kasuwanci inda aka tsayar da asusun ajiyar duk masu amfani da kafar ta yanda baza a iya tura ko karbar kudi ba har sai zuwa 14 ga watan Janairun 2017. Hakan ya jefa tsoro a zukatan mafi yawa daga cikin masu amfani da kafar duba da irin gargadin da babban bankin tarayya yayi kan cewar MMM yan damfara ne.
Sai dai kuma daga bisani shugaban gudanarwa na MMM Nigeria ya fito karara yayi wa jama'a bayanin cewa su harkarsu ba ta damfara ba ce face dai harka ce ta taimakawa juna.
Menene MMM kuma ya tsarin abun yake?
Na koma hutun semester a makaranta sai wani abokina yake tambayata cewar shin Deendabai kana yin MMM duba da cewar kakan yi kokarin shiga abubuwan da suka shafi hanyar juya kudi ta internet? Amsar da na bashi itace ban yarda da tsarin ba saboda haka bana yi.
MMM gajarcaccen bayanin wasu kalmomi ne na turanci da yake nufinMavrodi Mondial Moneybox, asusu ne na adashin kudi da ya faro daga kasar rasha(Russia), wanda ya kware wajen yin adashe na kudi tare da juyasu ta yanda kowanne member zai rika samun kudin ruwa bayan kwana talatin (30) da zuba kudinsa da karin kaso talatin (30%).
Yadda abun yake shine in ka zuba kudi a matsayinka na sabon mamba to za'a dauki kudinka a ba tsohon mamba da yakai akalla kwana talatin da zuba kudi, haka kaima za'a dauko kudin wasu sabbin mambobin tare da karin kaso 30 a baka bayan cikar kudinka da kwana talatin a gurinsu. Misali ace ka zuba kudi kamar naira dubu dari N100,000, to a tsarin MMM zaka karbi Naira dubu dari da talatin ne bayan kwana 30.
Sai dai kuma tsarin MMM yasha kakkausar suka musamman daga malamai duba da cewar harka ce da ta shafi bayarda kudin ruwa wanda hakan ya sabawa koyarwar addinin musulunci, dadin dadawa kuma akwai alamun cuta ko cutarwa a cikin lamarin bisa la'akari da cewar ba a san kowanne irin kasuwanci akeyi da wadannan kudade ba.
Wannan shine dan takaitaccen bayani dangane da MMM da zaku iya ji daga bakin Deendabai. Fatan zaku tura ma abokanen wannan labari don suma su karu...

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "MMM Nigeria Ya Dawo Aiki, Ko Menene Shi MMM Din?"

Post a Comment