MAN UNITED YAFI KOWANI CLUB SAMUN KUDIN SHIGA

Kamfanin Deloitte, wanda ke yin kididdiga kan yawan kudin da kulob-kulob ke samu ya ce kulob din Manchester United ya fi kowanne kulob samun kudin shiga a kakar wasan 2015-16.

United ya maye gurbin kulob din Real Madrid - wanda ya kwashe 11 a matsayin kulob din da ya fi samun kudin shiga.

United ya samu kudin shigar da suka kai £515m a kakar wasan ta 2015-16.
Talla

Kulob din ya samu karin £71m a kudin tallace-tallacen da yake karba.

Kudin shigar da kulob 20 mafiya karfin tattalin arziki suka samu a kakar wasa ta 2015-16 ya karu da kashi 12 inda suka samu £6.41bn, abin da ba su taba samu ba.

Wannan ne karon farko da kulob din Manchester United ya zamo na farko a jadawalin Deloitte Football Money League tun kakar wasa ta shekarar 2003-04.

Kulob din Real ya koma matsayi na uku, bayan Barcelona, wanda ya rike matsayinsa na biyu.

Bayern Munich ya matsa zuwa matsayi na hudu sannan Manchester City ya zama na biyar - inda ya samu kudin shiga £392.6m.

Takwas daga cikin kulob-kulob na gasar Premier na cikin kulob 20 da suka fi samun kudin shiga a bana, inda suka samu kusan £2.4bn.

Kulob din Champions Leicester City ya shiga jerin kulob 20 mafi karfin tattalin arziki a karon farko a tarihinsa, inda ya zamo na 20.

Ya samu kudin shigar da suka kai £128m, wato ninki biyar kan kudin da ya samu a kakar wasa ta 2013-14.

Arsenal, Chelsea, Liverpool da kuma Tottenham sun ci gaba da zama a matsayi na bakwai da na takwas da na tara da kuma na 12, yayin da West Ham ya zama na 18.
Jadawalin kudin shiga da Deloitte Money League ya fitar a kakar wasa ta 2015-16 - goman farko
Kulob-kulob (matsayin su a kakar wasan da ta wuce) Kudin shiga €m (£m a cikin baka) 2015-16 Kudin shiga 2014-15
1 (3) Manchester United 689 (515.3) 519.5 (395.2)
2 (2) Barcelona 620.2 (463.8) 560.8 (426.6)
3 (1) Real Madrid 620.1 (463.8) 577 (439)
4 (5) Bayern Munich 592 (442.7) 474 (360.6)
5 (6) Manchester City 524.9 (392.6) 463.5 (352.6)
6 (4) Paris St-Germain 520.9 (389.6) 480.8 (365.8)
7 (7) Arsenal 468.5 (350.4) 435.5 (331.3)
8 (8) Chelsea 447.4 (334.6) 420 (319.5)
9 (9) Liverpool 403.8 (302) 391.8 (298.1)
10 (10) Juventus 341.1 (255.1) 323.9 (246.4)

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "MAN UNITED YAFI KOWANI CLUB SAMUN KUDIN SHIGA"

Post a Comment