Koriya ta Arewa za ta gwada makamin ƙare- dangi

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya
ce kasarsa na dab da yin gwajin makaman kare-
dangi masu cin dogon-zango wadanda za su iya
daukar makamashin nukiliya.
Mr Kim, wanda ya bayyana haka a sakonsa na
sabuwar shekara, ya kara da cewa yanzu haka
ana gabar karshe ta kammala kera makaman.
Sau biyu Koriya ta Arewa ta yi gwajin makaman
nukiliya a shekarar 2016.
Hakan ya janyo fargabar cewa watakila kasar ta
sabunta shirinta na kera makaman na nukiliya.
Sai dai ba ta taba yin nasara a gwaje-gwajen da
ta yi na makaman ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato
wani babban jami'in rundunar sojin Amurka na
cewa duk da yake Koriya ta Arewa tana da karfin
kera kawunan makaman nukiliya amma ba za ta
iya harba su domin cin dogon-zango ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Koriya ta Arewa za ta gwada makamin ƙare- dangi"

Post a Comment