Mutane 4 sun mutu a hari da babbar mota a Jerusalem

Wani Bafalasdine ya kashe 'yan kasar Isra'ila
hudu a Jerusalem lokacin da ya danna da
babbar mota cikin wani gungun sojojin, a wani
abu da 'yan sanda suka ce hari ne na ta'addanci.
Wadanda suka mutun sun hada da mata uku da
namiji guda, sannan wasu goma sha uku kuma
sun jikkata.
'Yan sanda sun ce sojojin dake kusa sun harbe
direban har lahira.
A watanni goma sha biyar da suka gabata,
mutane daga Falasdinu sun sha kai hare hare da
wuka da bindiga da kuma motoci akan 'yan
Isra'ila.
Babban jami'in 'yan sandan Isra'ila, Roni Alsheich
ya ce maharin na ranar Lahadin nan, Bafalasdine
ne daga Gabashin Jerusalem.
Bidiyon da kyamarorin gefen hanya suka nada,
ya nuna babbar motar lokacin da take tafiya a
guje inda ta danna cikin sojojin, sannan kuma
direban ya koma da baya inda ya sake bi ta kan
mutanen da ya taka.
Kafin harin na ranar Lahadi, Isra'ilawa talatin da
biyar aka kashe a hare-haren da ake zargin
Falasdinawa ko Larabawan Isra'ila da kai wa tun
daga watan Oktoban 2015.
Isra'ila ta ce Falasdinawa fiye da dari biyu ne,
akasarinsu maharan, aka kashe a lokacin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mutane 4 sun mutu a hari da babbar mota a Jerusalem"

Post a Comment