Buhari ya yi kira ga 'yan Shi'a su zauna lafiya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya
bukaci 'ya'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi
wadanda aka fi sani da 'yan Shi'a da su rungumi
turbar zaman lafiya.
Shugaban ya bayyana haka ne a sakonsa na
sabuwar shekara.
Shugaba Buhari ya ce, "A matsayinsu na 'yan
uwanmu, muna kira ga 'yan Shi'a su rungumi
turbar zaman lafiya. Dole su bi dokokin kasar da
suke zaune a ciki".
Ya kara da cewa, "A lokaci guda kuma, dole
jami'an tsaro su rika mu'amala da su ta hanyoyin
da suka dace da kuma bin doka kan yadda suke
tunkararsu".

Hakan na zuwa ne dai a yayin da 'yan Shi'a ke ci
gaba da korafi kan zargin gallazawar da jami'an
tsaron kasar ke yi musu.
Hukumomin kare hakkin dan adam irin su
Amnesty International sun ce jami'an tsaron na
Najeriya sun kashe daruruwan 'yan Shi'a a
lokacin da suka bude musu wuta a birnin Zaria a
watan Disambar shekarar 2015.
Bayan haka ne suka kama shugaban kungiyar
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da wasu
manya-manyan 'yan kungiyar inda har yanzu
suke ci gaba da tsare su duk da hukuncin da
kotu ta yanke na sakin su.
'Zaman lafiya a Naija Delta'
Shugaba Buhari ya kuma ce zai ci gaba da
neman zaman lafiya da mazauna yankin Naija
Delta mai arzikin man fetur.
A cewarsa, "ina jaddada kira ga 'yan uwana na
yankin Naija Delta wadanda suke tayar da kayar-
baya da kuma yin zagon-kasa ga tattalin arzikin
kasa da su zo mu sasanta."
Sai dai shugaban na Najeriya ya ce za su tunkari
duk wani mutum da ba ya kaunar zaman lafiya,
yana mai shan alwashin cewa ba zai bar wani ko
wata su durkusar da Najeriya ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Buhari ya yi kira ga 'yan Shi'a su zauna lafiya"

Post a Comment