Cutar mantuwa ta fi kama masu zama daf da titi — Bincike

Wani bincike da aka wallafa a mujallar Lancet
ta Burtaniya ya ce mutanen da ke zama daf da
titi sun fi shiga hatsarin kamuwa da cutar
kidimewa.
Kimanin kashi 11 cikin 100 na masu fama da
cutar mantuwa da ke zaune cikin mita 50 daga
babban titi na da alaka da hada-hadar abubuwan
hawa, a cewar binciken.
Masu binciken - wadanda suka bibiyi rayuwar
mutum miliyan biyu a Kanada tsawon shekara 11
- sun ce gurbatacciyar iska da hayaniyar ababen
hawa ka iya sa dakushewar kwakwalwa.
Kwararru a kan cutar mantuwa a Burtaniya sun
ce akwai bukatar kafa hujja don tabbatar da
bincike, ko da yake yana da "kanshin gaskiya".
' Karuwar Jama'a'
Kimanin mutum miliyan 50 ne ke fama da cutar
mantuwa a duniya, kuma ba a iya gano
abubuwan da ke raba mutane da tunani da kaifin
kwakwalensu ba.
Binciken ya gano mutum 243,611 da ke fama da
cutar cikin mutum miliyan biyu, amma wadanda
suka fi hatsarin kamuwa da ita na rayuwa ne daf
da manyan tituna.
Masu binciken sun kuma yi la'akari da karin wasu
sabubba irin su fatara da taiba da matsayin ilmi
da shan taba wajen janyo cutar mantuwa.
Shawara mafi alheri don rage kasadar kamuwa
da cutar mantuwa shi ne yin abubuwan da muka
san suna inganta lafiyar jiki - daina shan tabar
sigari, motsa jiki da cin lafiyayyen abinci.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Cutar mantuwa ta fi kama masu zama daf da titi — Bincike"

Post a Comment