Dokar Nigeria ta durkusar da kasuwar motoci a Jamhuriyar Benin

Masu sayarda motoci a Cotonou babban birnin
jamhuriyar Benin, sun koka da rashin cinikin
motoci, tun bayan da gwamnatin Najeriya ta
sanar da hana shigo da motoci na tokumbo daga
iyakokinta na tudu.
Bincike ya nuna cewa sama da kaso casa'in da
biyar na motocin tokumbo da ake sauke su a
gabar tekun jamhuriyar Benin, masayansu na
fitowa daga Nigeria ne mai makwabtaka da
kasar.
Masu sayar da motocin sun ce yanzu kasuwar ta
ja baya kuma farashin motocin ya sauko, saboda
faduwar darajar Naira da kuma rufe iyakokin da
Nigeriar ta yi wadanda suka taimaka wajen
rashin samun cinikin motocin.
A baya dai jiragen ruwa na sauke kwantenoni
ciki da motoci kamar dubu goma a wata,amma
tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da
sabuwar dokar,jirage a gabar tekun Cotonou suka
ja baya inda a sati bai fi a sauke kwantenoni
hamsin ba.
Rasa ayyuka
Karancin masu sayen motocin ya sanya wasu
daga cikin masu wannan harakar rasa
ayyukansu.
Majalisar Dattawan Nigeriar dai ta bukaci
gwamnatin kasar da ta janye wannan matakin da
ta ce ya haddasa dubban 'yan kasar sun rasa
aikin yi.
To sai dai kuma hukumar hana fasakwauri ta
Nigeria ta ce matakin da aka dauka zai taimaka
wajen bunkasa harajin da gwamnati ke samu
tare da samar da aikin yi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Dokar Nigeria ta durkusar da kasuwar motoci a Jamhuriyar Benin"

Post a Comment