Nigeria: Majalisar dattawa za ta yi bincike a kan rikicin Kaduna
Majalisar dattawan Najeriya ta ce za ta gudanar
da bincike a kan musabbabin rikicin da ake
fama da shi a kudancin jihar Kaduna da nufin
samar da maslaha.
Wasu daga cikin al`umomin yankin dai sun ba da
shawarar cewa ya kamata a yi amfani da
shawarwarin da wasu kwamitoci suka ba wa
wasu gwamnatocin da aka yi a jihar a baya,
maimakon a kwashe wani lokaci ana yin sabon
bincike.
Senata Shehu Sani dan majalisar dattawa ne
daga jihar Kaduna, ya kuma shaidawa BBC
cewa,an gabatar da wani kuduri a gaban
majalisar wanda ya nemi ayi bincike domin a
gano wadanda suke da hannu a kan wannan
rikici, sannan kuma a gano wadanda rikicin ya
shafa, da kuma fito da hanyoyi na tsaro ta yadda
za a magance afkuwar irin wadannan tashe-
tashen hankulan a gaba.
Sanata Shehu Sani, ya kuma ce za a duba aga
irin taimakon da gwamnati za ta yiwa wadanda
irin wannan rikici ya shafa.
Wannan ne dai karon farko da majalisar dattawan
za ta shiga cikin wannan batu domin ganin an
kawo karshen wannan rikici da ke faruwa a
kudancin Kaduna.

0 Response to "Nigeria: Majalisar dattawa za ta yi bincike a kan rikicin Kaduna"
Post a Comment