Nigeria: An sake gano wata 'yar Chibok
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun
sake gano wata yarinya daga cikin 'yan matan
Chibok fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka
sace fiye da shekara biyu da ta gabata.
Yarinyar mai suna Rakiya Abubakar, an gano ta
ne tare da jaririnta dan wata shida a yankin
Alagarno a jihar Borno.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta ce
yarinyar na samun kulawar jami'an kiwon lafiya
kafin a mika ta ga gwamnatin jihar ta Borno.
Ta kara da cewa an gano yarinyar ce a lokacin
da ke bincikar wasu da aka kama bisa zargin
suna da alaka da Boko Haram.
Fiye da shekara biyu kenan da aka sace yaran su
276 daga makarantarsu a garin Chibok, lamarin
da ya ja hankalin duniya sosai.
A watan Oktoban da ya wuce aka sako wasu 21
daga cikinsu bayan wata jarjejeniya da aka
cimma da kungiyar ta Boko Haram.
Sai dai har yanzu da dama daga cikinsu na
hannun 'ya'yan kungiyar.
Boko Haram'
A baya-bayan nan dakarun tsaron Najeriya da na
makwaftan kasashe na samun nasara kan
mayakan Boko Haram.
Amma har yanzu kungiyar na ci gaba da kai
hare-hare musamman na kunar bakin wake.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce tana na
cigaba da farautar 'yan Boko Haram din, kuma a
yanzu ta fatattake su daga sansaninsu da ke
dajin Sambisa.
0 Response to "Nigeria: An sake gano wata 'yar Chibok"
Post a Comment