El-Zakzaky: 'Yan Shia sun bukaci Buhari ya bi umarnin kotu

Kungiyar 'yan uwa Musulmi w
adda aka fi sani da
Shi'a ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu
Buhari ya saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-
Zakzaky kamar yadda kotu ta ba shi umarni
maimakon kiran da ya yi musu na su zauna
lafiya.
A jawabinsa na sabuwar shekara Shugaba Buhari
ya ce, "A matsayinsu na 'yan uwanmu, muna kira
ga 'yan Shi'a su rungumi turbar zaman lafiya.
Dole su bi dokokin kasar da suke zaune a ciki".
Ya kara da cewa, "A lokaci guda kuma, dole
jami'an tsaro su rika mu'amala da su ta hanyoyin
da suka dace da kuma bin doka kan yadda suke
tunkararsu".
Sai dai a wata sanarwa da kakakin kungiyar
Ibrahim Musa ya aike wa manema labarai, ya ce
Shugaba Buhari shi ne mutumin da ba ya bin
dokokin Najeriya domin kuwa sau da dama kotu
na bayar da umarnin a saki Sheikh El-Zakzaky
amma har yanzu gwamnatin kasar ta ki yin
biyayya ga hukuncin kotun.
'Ba ya yin biyayya ga kotu'
Ya kara da cewa, "Shugaban kasa, har yanzu ba
ka bi umarnin kotu ba na sakar shugabanmu,
Sheikh Ibraheem Zakzaky, wanda aka tsare ba
bisa ka'ida ba kuma ba tare da an tuhume shi
ba, fiye da shekara daya duk da umarnin da kotu
ta bayar na yin hakan."
Sanarwar ta ce, "Ko a makon jiya lauyanmu Femi
Falana (SAN) ya rubuta maka [Buhari] wasika
inda ya yi maka tuni a kan hakan ta hannun
ministan shari'a. Don haka ya kamata ka yi
biyayya ga dokokin kasa ta hanyar bin umarnin
kotu ka saki Sheikh Zakzaky ba tare da bata
lokaci ba".
Ibrahim Musa ya ce matakin da suka dauka na
zuwa kotu duk da cin zarafin da dakarun tsaron
Najeriya suka yi mus ya nuna cewa kungiyarsu
tana matukar kaunar zaman lafiya sabanin
kashin-kajin da ake shafa mata cewa ita mai son
tayar da zaune tsaye ne.
Sanarwar ta yi kira ga Shugaba Buhari ya saki
dukkan 'ya'yan kungiyar da ake tsare da su tun
bayan dirar-mikiyar da aka yi musu a birnin Zaria
a watan Disambar shekarar 2015, kana a hukunta
jami'an tsaron da suka kashe 'yan kungiyar a
Zaria, Kaduna, Kano, Funtua da kuma Sokoto.
Hukumomin kare hakkin dan adam irin su
Amnesty International sun ce jami'an tsaron na
Najeriya sun kashe daruruwan 'yan Shi'a a
lokacin da suka bude musu wuta a birnin na
Zaria bayan sun zarge su da yunkurin kashe
shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar
Yusuf Tukur Buratai, zargin da suka sha
musantawa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "El-Zakzaky: 'Yan Shia sun bukaci Buhari ya bi umarnin kotu"

Post a Comment