'Nigeria za ta fuskanci matsala idan ta rufe filin jirgin Abuja'

Kungiyar masu kamfanonin jiragen sama a
Najeriya ta cewa akwai yiwuwa a fuskanci cikas
a zirga-zirgar jiragen sama da zarar gwamnatin
tarayya ta rufe filin jirgin saman Abuja.
A watan jiya ne dai ma'aikatar kula da sufurin
jiragen saman kasar ta ce za a rufe filin tsawon
makonni shida domin a yi gyare-gyaren a tituna.
Ta ce za a karkatar da tashi da kuma saukar
jiragen saman zuwa Kaduna.
Sai dai wani babban jami'in jiragen sama na Arik
Airline, Captain Ado Sanusi, ya shaida wa BBC
cewa koda yake suna goyon bayan matakin
amma suna so a yi taka-tsantsan.
Ya kara da cewa, "Yawancin lokuta idan an ce za
a yi gyaran filin jirgin sama na wata uku zuwa
hudu yana kai wa shekara daya zuwa biyu. Kuma
anya Kaduna tana da wurin da za a iya ajiye man
jirgin sama? Mun yi magana da masu ba mu man
jirgi kuma sun ce Kaduna ba ta da karfin da za
ta iya ajiye mai da yawa."
Captain Sanusi ya nemi gwamnati ta sake duba
wannan mataki, yana mai cewa a kullum suna
sauke jirage sama da 80 a Abuja kuma ba su da
tabbacin cewa filin jirgin saman Kaduna zai iya
daukar wannan dawainiya.
Da ma dai wasu masu ruwa da tsaki a sufurin
jiragen saman na fargabar sauke fasinjoji a
Kaduna, musamman ganin cewa hanyar Abuja
zuwa Kaduna na fama da barayin mutane domin
karbar kudin-fansa.
Sai dai ministan sufurin jiragen saman Hadi
Sirika ya ce za su dauki matakan tsaro a kan
hanyar, yana mai cewa gyara titin jirgin saman
na Abuja na da matukar muhimmanci.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Nigeria za ta fuskanci matsala idan ta rufe filin jirgin Abuja'"

Post a Comment