Amurka: An kama mutane 4 kan saka wani bidiyo a Facebook

An kama wasu matasa hudu a jihar Illinois ta
Amurka bayan saka wani video a shafin internit
da ke nuna wani farar fata daure ana azabtar da
shi.
'Yansandan Amurkar sun ce suna bincike kan
lamarin wanda ya faru a Chicago - abin da ya sa
aka kama matasan maza biyu da mata biyu -
bisa zargin nuna kiyayya ga wani jinsi.
A cikinsa an ga wani saurayi dan shekaru 18
yana neman ceto a kusurwar wani daki an rufe
masa baki, an daure masa hannuwa da kafafu,
ga kuma alamun yankan wuka a kansa.
A gefe guda kuma aka ga wadannan matasa
bakar fata tsaye suna dariya, suna zukar sigari
kuma suna yin wasu kalaman batanci ga fararen
fata musamman shugaban kasar mai jiran gado
Donald Trump.
Bullar wasu karin faya-fayai
Wasu fayafayan bidiyon da aka saka a shafukan
internet daga bisani sun nuna yadda aka lakada
wa matashin duka, aka sa yasa ruwa daga kasko
bawali, kuma aka tilasta masa ya ce ''ina kaunar
bakaken fata.''
Masu bincike sun ce wanda aka ci wa zarafin
abokin daya daga cikin wadan da suka yi masa
wannan aikin ne kuma ga alamu sun tsare shi a
wurin har tsawo kwana biyu.
Bincikensu ya soma ne bayan an gane shi yana
tambele a kan titunan birnin Chicago cikin wani
hali na matukar bukatar agaji.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Amurka: An kama mutane 4 kan saka wani bidiyo a Facebook"

Post a Comment