Nigeria: Ko Donald Trump zai goyi bayan kafa kasar Biafra?

Tun dai bayan zaben shugaba Muhammadu
Buhari a bara, dangantakar Najeriya da Amurka
ta dan inganta.
Dangantakar dai ta yi tsami ne bayan zargin cin
zarafin bila'dama da ake yiwa sojojin Najeriyar,
musamman ma a yakin da suke yi da mayakan
Boko Haram.
Sojojin Najeriyar suna samun horo da kuma
kayan aiki daga gwamnatin Barack Obama, don
haka za su so Mista Trump ya ci gaba da karfafa
wannan dangantakar.
Najeriya za ta kuma so ta samu kyautatuwar
dangantakar kasuwanci da Amurkar.
Wasu daga cikin manyan kamfanonin Amurka na
cikin gaggan masu zuba jari a bangaren
makamashi a Najeriya, amma kuma gano danyan
man da Amurkar ta yi ya sa yawan man da ta ke
saya daga kasar ya ragu.
Me ya sa shugabannin Afirka ke tsoron
mulkin Trump?
'Katobarar da Donald Trump ya yi'
Su waye na hannun-daman Trump
'Yan aware na Biafra
Me yiwuwa kasashen biyu su samu kan su cikin
yanayin nan da Hausawa ke kira ta ciki-na-ciki,
ko kuma akai ruwa-rana, muddin Mista Trump ya
yanke shawarar amincewa da 'yan awaren
Biafra.
Masu fafitikar ballewa daga Najeriyar sun nuna
goyon bayansu ga dan takarar jam'iyyar
Republican din a lokacin yakin neman zabe, suna
masu fatan cewa zai goyi bayan fafitikar da suke
yi ta samun wannan 'yancin.
Sun ce ya goyi bayan ''Brexit''- matakin Birtaniya
na ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai - don
haka suke ganin zai goyi bayan "Biafrexit", koda
yake bai nuna alamun zai yi hakan ba a bainar
jama'a.
An samu hargitsi tsakanin masu fafitikar kafa
kasar Biafra da jami'an tsaro a lokacin da suke
zanga-zangar nuna goyon baya a ranar da aka
rantsar da Shugaba Trump.
Wasu rahotanni sun ce an samu asarar rayuka
amma jami'an 'yan sanda sun ce babu wanda ya
mutu.
Akwai 'yan Najeriya fiye da miliyan daya da ke
zaune a Amurka, kuma wasu na fargabar cewa
manufofin Mista Trump kan harkokin shige-da-
fice ka iya kai wa ga korar dubban su zuwa gida.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Ko Donald Trump zai goyi bayan kafa kasar Biafra?"

Post a Comment