Myanmar ta ce babu shaidar an yi wa Musulmi kisan kiyashi

Wani kwamitin bincike a Myamar ya ce har
yanzu bai samu wata hujja da ke nuna cewa an
yi wa musulman kasar 'yan kabilar Rohingya
kisan kiyashi a jihar Rakhine ba.
A rahotonsa na wucin-gadi, kwamitin ya ce babu
isasshiyar hujjar da ta tabbatar da zarge-zargen
cewar fyade ya zama ruwan-dare a yankin.
Sai dai kwamitin bai ce komai ba a kan zarge-
zargen da aka yi wa jami'an tsaro na kashe
mutane.
An yi ta rade-radin cewar ana musguna wa 'yan
kabilar Rohingya tun lokacin da sojojin kasar
suka fara yaki da 'yan tada-kayar-baya a watan
Oktoban da ya wuce.
Wasu sun bayyana matakin dakarun kasar a
matsayin kisan kare-dangi, jogarar kasar ta
Myanmar, Aug San Suu Kyi, ta fuskanci suka
daga kasashen duniya.
Kwamitin, wanda wani tsohon sojan kasar Janar
Myint Swe ke jagoranta, zai kammala rahotonsa
kafin karshen watan Janairu.
Kwamitin ya ce har yanzu akwai musulmai 'yan
kabilar Rohingya wadanda suke zama a Rakhine
kuma ba a lalata masallatai da makarantu ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Myanmar ta ce babu shaidar an yi wa Musulmi kisan kiyashi"

Post a Comment