PDP ta yi Allah wadai da korar 'yan sanda 6 a Najeriya

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta PDP ta yi Allah
wadai da matakin da rundunar 'yan sandan kasar
ta dauka na sallamar jami'anta shida dake aiki
da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada
labaranta na kasa, Prince Dayo Adeyeye ya fitar,
jam'iyyar PDP ta ce shari'ar da aka yi wa 'yan
sandan a asirce, da kuma sallamarsu da aka yi,
abu ne na rashin gaskiya.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa, saurin korar 'yan
sandan da aka yi, wata karin alamace ga
yunkurin yin magudi da halaka gwamna Wike
gabanin zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar
Rivers a watan Disamba.
Jam'iyyar PDP ta ce "gwamnatin APC ta yanke
shawarar hukunta jami'an 'yan sandan ne saboda
sun dage yin aikinsu yadda ya kamata, sun ki
aiwatar da shirin wasu na ganin bayan gwamna
Wike".
Ta kuma kara da cewa zargin saba ka'idojin aiki
da ake wa 'yan sandan, wani abin kunya ne ga
tsarin aikin dan sanda da tafarkin dimukradiyya.
A saboda haka jam'iyyar ta PDP ta yi kiran ganin
an mayar da 'yan sandan bakin aikinsu ba tare da
bata lokaci ba, domin kare martabar aikin, da
gaskiya da adalci.
In za a tuna, rundunar 'yan sandan Najeriya ta
sallami jami'an na ta shida ne wadanda ta ce sun
aikata laifuka daban-daban a lokacin zaben 'yan
majalisu da aka gudanar a jihar Rivers.
Kakin rundunar Don Awunah ya ce bincike ya
nuna cewa jami'an wadanda suka hada da Sufeto
Eyo Victor da Sajen Peter Ekpo da Sajen Ogoni
Goodluck sun yi harbi cikin jama'a ba bisa ka'ida
ba.
Sauran sun hada da Sajen Orji Nwoke da Sajen
Okpe Ezekiel da kuma Sajen Tanko Akor.
Ta kara da cewa sun aikata laifin ne ranar 10 ga
watan Disambar 2016 lokacin da suka bi tawagar
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, wajen dirar
mikiya a kan sakatariyar karamar hukumar
Fatakwal.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "PDP ta yi Allah wadai da korar 'yan sanda 6 a Najeriya"

Post a Comment