Kun san abin da zai sa tsofaffi su riƙa jin daɗin bacci?

Masana kimiyya sun shawarci mutanen da suka
kai shekara 50 zuwa sama da su kauracewa
shan gahawa ko kofi bayan cin abincin rana idan
dai suna so su yi bacci mai dadi da daddare.
Wani rahoto da kungiyar masana kan lafiyar
kwakwalwa ta charity Age da ke Birtaniya ta fitar
ya ce samun bacci mai dadi yana yi wa tsofaffi
wahala amma samun isasshen hutu zai taimaka
wa kwakwalwarsu ta rika tunani mai kyau.
Rahoton ya bai wa tsofaffi shawara su rika yin
baccin awa bakwai zuwa takwas da daddare,
sannan suka fitar da hanyoyin da suke gani idan
an bi su za a tabbatar da hakan.
Baya ga daina shan gahawa, rahoton ya bukaci
tsofaffi su takaita kalular da suke yi da rana
zuwa kasa da awa daya.
Sauran shawarwarin su ne:
Su rika tashi daga bacci a lokaci daya
kowacce rana
Su rika shan hantsi
Kada su sha giya
Su ci abincin dare awa uku kafin su yi bacci
Kada su rika karatu ta kwamfuta ko wayar
salula ko kwamputar tebur kafin su kwanta
bacci
Su gujewa yin amfani da magungunan da ba
likita ne ya ce a yi amfani da su ba
Su rika sanya safa a kafafunsu kafin su yi
bacci
Kada su yi bacci tare da daddobin gida irin
su kyanwa
Su gujewa yin musu da matarsu ko
mazajensu kafin su kwanta

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kun san abin da zai sa tsofaffi su riƙa jin daɗin bacci?"

Post a Comment