Jiragen yakin Nigeria sun kashe 'fararen hula 50' bisa kuskure

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta
hallaka tare da jikkata fararen hula bisa kuskure
a kauyen Rann, da ke Kala Balge a jihar Borno.
Kungiyar likitocin sa kai ta MSF ta ce mutane
akalla 50 ne suka mutu, yayin da 100 suka
jikkata.
Ma'aikatan agaji na cikin wadanda suka samu
raunuka - kungiyar bada agaji ta Red Cross ta
tabbatar da mutuwar shida daga cikin
ma'aikatanta.
Harin ya faru ne a kauyen Rann da ke kusa da
kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda sojoji ke
fafatawa da mayakan Boko Haram.
Wani kwamanda a rundunar sojin Najeriya Manjo
Janar Lucky Irabor ya ce matukin jirgin yakin ya
kai hari kan mutanen ne a bisa kuskuren cewa
'yan Boko Haram ne.
Ya ce an bashi umarni ne a bisa bayanan sirri
game da wuraren taruwar mayakan Boko Haram.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike
da sakon nuna takaici da kuma jaje, game da
asarar rayukan da aka yi, ya kuma yi kira da a
kwantar da hankali.
Kakakin fadar shugaban kasar, ya ce gwamnati
za ta tallafawa gwamnatin jihar Borno game da
wannan abin bakin ciki da ya faru.
Kakakin kungiyar MSF Etienne l'Hermitte ya yi
kira ga mahukuntan Najeriya da su taimaka
wajen kwashe mutanen da suka samu raunuka ta
sama da ta kasa.
"Jami'an kiwon lafiyarmu a kasashen Kamaru da
Chadi a shirye suke su duba wadanda suka
jikkata", in ji shi.
MSF ta ce akasarin wadanda harin ya rutsa da
su mutanen da suka gudu daga matsugunansu
ne a yankunan da 'yan Boko Haram ke kai hare-
hare.
Rahotanni sun ce lamarin dai ya rutsa da jami'an
tsaro da dama, inda wasu suka mutu yayin da
wasu kuma suka samu raunuka.
Rundunar sojin ta ce tana amfani da jirage masu
saukar ungulu domin kwashe wadanda suka
jikkata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jiragen yakin Nigeria sun kashe 'fararen hula 50' bisa kuskure"

Post a Comment