Ana shirin jibge bataliyar soji 2 a kudancin Kaduna

Rundunar Sojin Nigeria na shirin girke karin
bataliyar soji biyu a kudancin jihar Kaduna
domin dakile wutar rikicin kabilanci da addini da
ta ki ci ta ki cinyewa a can.
Wannan na daga cikin matakan da Shugaban
kasar Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a
dauka da manufar kawo karshen salwantar da
rayukka da dukiyoyin jama'a da ake ci gaba da yi
a can - kamar yadda wata sanarwa daga fadarsa
ta bayyana.
Sanarwar ta ce wannan kari ne bisa ga kafa
wata rundunar 'yansandan kwantar da tarzoma
da aka yi a yankunan da ake saurin samun
rikicin.
Haka ma shugaban kasar ya umarci hukumar
bayar da agajin gaggawa ta kasar wato Nema;
da ta yi nazari kan halin da ake ciki domin sanin
irin daukin da za a kai wa wadanda rikicin ya
rutsa da su.
Rayukka da dukiyoyi masu dimbin yawa ne ke
salwanta a yankin sakamakon hare-hare masu
alaka da kabilanci da addini da ke faruwa lokaci
zuwa lokaci.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana shirin jibge bataliyar soji 2 a kudancin Kaduna"

Post a Comment