Ana ci gaba da Ja-in-ja tsakanin Obama da Trump kan Obamacare

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga
'yan majalisar dokokin kasar daga jam'iyyarsa ta
Demokrat da su tashi haikan su kare tsarin
inshorar kiwon lafiyar da gwamnatinsa ta fito da
shi; wanda gwamnatin Trump ta sha alwashin
soke wa.
A cikin wata ganawa ta sa'oi biyu da 'yan
majalisar ranar Laraba, Mr. Obama ya nemi
goyon bayan 'yan jam'iyyar tasa kan su hana 'yan
Refublika kawar da wannan tsarin nasa.
Ganawar ta biyo bayan da mataimakin shugaban
kasar mai jiran gado, Mike Pence, ya je majalisar
inda ya shaida wa 'yan jam'iyyarsu ta Refublika
cewa gwamnatinsu za ta sauya wannan tsarin.
Bayan ziyarar da shugaban barin gado ya kai
harabar majalisar, dan majalisar wakilai na
jam'iyyar Demokrat Elijah Cummings ya shaida
wa manema labarai cewa Mr. Obama ya nemi da
su tashi haikan su kare wannan manufar tasa.
Wadannan kalaman nasa sun zo ne bayan da
'yan jam'iyyar ta Refublika da ke majalisar
dattawa suka dauki matakin farkon na soke
tsarin kiwon lafiyar da aka fi sani da Obamacare.
Sun jefa kuri'a amincewa da wani kuduri a
kasafin kudi da aka tsara da manufar zaftare
kudade ake warewa tsarin.
Wannan tsarin kiwon lafiyar dai ya fadada
hanyoyin samun inshorar kiwon lafiya ga
Amurkawa Miliyan 20 wadanda ba su iya
samunsa in ba don tsarin ba.
Amma tsarin - wanda aka fito da shi tun a
shekara ta 2010 - ya gamu da cikas na karuwar
tsadar kudaden da ake biya da kuma janyewar
manyan kamfanonin da ke bayar inshorar ta
lafiya, abin da ya bar Amurkawan da zabi maras
yawa kan kiwon lafiya.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Ana ci gaba da Ja-in-ja tsakanin Obama da Trump kan Obamacare"

Post a Comment