Cacar-baka tsakanin gwamnati da BBOG kan Sambisa

Gayyatar da gwamnatin Najeriya ta yi wa 'yan
kungiyar da ke fafutikar ganin an ceto 'yan
matan Chibok, wato BBOG, zuwa dajin Sambisa
ta janyo zazzafar muhawara.
Ita dai gwamnatin, a wata takardar gayyata da
Ministan watsa labarai Lai Mohammed ya aikewa
kungiyar, ta yi kira ga 'yan BBOG su aike mata
da sunayen mambobinsu uku domin a tafi da su
Dajin Sambisa su ga irin fafutukar da ake yi ta
ceto 'yan matan na Chibok.
A cikin sanarwar, ministan ya yaba wa 'yan
kungiyar ta BBOG bisa fafutukar da suke yi, yana
mai cewa, "Domin jinjinawa fafatukar da kuke yi
don ganin an ceto 'yan matan Chibok, muna so
ku ba mu sunayen mambobinku uku domin zuwa
yankin arewa maso gabas ranar Litinin, 16 ga
watan Janairu".
A cewar Minista Lai Mohammed za a yi tafiyar
ne da ministan tsaro, da na watsa labarai, da
wasu 'yan jarida da babban hafsan sojin kasa, da
kuma babban hafsan sojin sama. Da farko
tawagar za ta fara zuwa Yola don ganin yadda
rundunar sojin sama ke farautar 'yan matan na
Chibok, sannan daga bisani su shiga jiragen
saman yakin da ke shawagi a Dajin Sambisa.
'Wasan-ɓuya'
Sai dai a wata wasikar martani da ta aike wa
ministan, kungiyar ta ce mabobinta sun gana sun
kuma yarda da yin amfani da irin wannan dama
don sanin halin da ake ciki a yankin na arewa
maso gabashin Najeriya.
Amma, a cewar wasikar, "Kafin a yi batun
tafiyar, ya kamata mu yi taro da ku domin ku
amsa mana wasu tambayoyi da ke damun mu.
Muna so mai bai wa shugaban kasa shawara a
kan sha'anin tsaro da ministan tsaro da babban
hafsan sojin kasa da kuma babban hafsan sojin
sama su halarci taron".
Kungiyar ta yi korafin cewa kwanaki kadan da
suka gabata wata kungiya da ta rika cin
mutuncin su ta samu tarba ta musamman daga
babban hafsan sojin kasa na Najeriya, lamarin
da, a cewar ta, yake matukar damun ta.
Ta kara da cewa dole ne babban hafsan sojin ya
nemi gafara daga wurinta sannan ya wanke
kansa daga cin zarafin da kungiyar ta yi musu
idan ana so su amsa goron gayyar gwamnati.
Daga bisani kuma daya daga cikin jagororin
kungiyar, Aisha Yesufu, ta wallafa a shafinta na
Twitter cewa tana kalubalantar shugaban kasar,
Muhammadu Buhari, ya jagorance su zuwa dajin
na Sambisa idan da gaske ne yake yaki da
ta'addanci.
Batun dai ya sa wasu na ganin 'yan kungiyar ta
BBOG suna kokarin guje wa gayyatar da aka yi
musu ne kawai, inda wasu ma ke ganin da ma
fafatukarsu ba ta wuce Abuja, fadar gwamnatin
kasar, ba.
Sai dai wasu sun ce ba haka batun yake ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Cacar-baka tsakanin gwamnati da BBOG kan Sambisa"

Post a Comment