Gambia: Shugaba Jammeh ya sha alwashin ci gaba da mulki

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya sha
alwashin cewa 'zai zauna a kan kujerar mulki har
sai an yanke hukunci a kan sakamakon zaben
shugaban kasar'.
Shugaba Jammeh ya ce ba zai sauka daga
kujerar mulki ba sai bayan Kotun Koli ta yanke
shawara a kan jayayyar da yake yi da sakamakon
zaben, karar da sai a watan Mayu za a saurare
ta.
A wani jawabi da ya yi ta gidan talibijin na kasar,
ya jaddada rashin amincewa da katsalandan din
da kasashen waji ke yi a harkar cikin gida ta
kasar.
Wata tawagar ECOWAS a karkashin jagorancin
shugaban kasar Nijeriya za ta kai ziyara Gambia
ranar Juma'a don kara matsawa Yahya Jammeh
lamba don ya mika mulki ga Adama Barrow
bayan zaben watan Disamban bara.
Shugaba mai jiran gado Adama Barrow ya ce za
a kaddamar da shi a mako mai zuwa.
Mista Jammeh, wanda ya kwashe shekaru yana
mulki, da farko dai ya amince ya mika mulki
bayan an kayar da shi a zaben, sai dai kuma
daga bisani ya ce bai amince da sakamakon ba
saboda wasu kurakurai da aka ce an gano wajen
hada alkaluman.
Amma hukumar zaben ta jaddada cewa kuskuren
bai shafi sakamakon ba kuma Mista Barrow ne
ya lashe zaben.
Tun 1994 Mista Jameh ke mulkin kasar Gambia,
kuma ana zargin shi da tauye 'yancin bil'Adama
duk da cewa yana gudanar da zabe a-kai-a-kai.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Gambia: Shugaba Jammeh ya sha alwashin ci gaba da mulki"

Post a Comment