Nigeria: Shirin tallafin 5,000 duk wata ga talakawa ya fara aiki

Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara bayar da
tallafin Naira 5,000 ga matalauta miliyan daya a
sassan kasar daban daban.
Shirin wanda aka fara a jihohi tara, wani bangare
ne na yunkurin tallafawa marasa galihu da
Shugaba Muhammadu Buhari da jami'aiiyar APC
suka yi a lokacin yakin neman zabe.
Wata sanarwa da mai magana da yawun
mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya fitar
ta ce an biya kudin ne ta wani tsari na
musamman da gwamnatin tarayya ta kirkiro dan
tallafawa mabukata.
Sanarwar ta ce 'yan Najeriya miliyan daya ne za
su ci gajiyar shirin, inda za su din ga karbar
tallafin a kowanne wata, kamar yadda ya ke a
cikin kasafin kudin bara.
Mista Akande ya ce tuni wasu daga cikin 'yan
kasar suka tabbatar da fara karbar tallafin kudin
tun a makon da ya wuce, a lokacin da shirin ya
fara aiki.
''Rukunin farko sun karbi kudaden a jihohin kasar
nan tara a ranar Juma'ar karshe ta watan
Disamba, kuma nan da ba da jimawa ba za a bai
wa sauran jihohi biyar na su kudin dan cike
gurbin rukunin farko na shirin'', in ji shi.
Jihohin da suka fara karbar tallafin sun hada da
jihar Borno, Kwara, Cross Rivers, Niger, Kogi,
Oyo, Ogun da kuma Ekiti.
Sai dai wasu masu sharhi na ganin zai yi wuya a
iya tantance mabukatan ganin cewa babu wani
cikakken kundin ajiye bayanai a kasar.
Amma Mista Akande ya ce an fara da wadannan
jihohi ne saboda gwamnatocinsu na da kididdigar
mutanen da ba su da karfi da ya kamata su
samu tallafin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: Shirin tallafin 5,000 duk wata ga talakawa ya fara aiki"

Post a Comment