Nigeria: An sallami 'yan sanda shida kan zaben Rivers

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sallami
jami'anta guda shida wadanda ta ce sun aikata
laifuka daban-daban a lokacin zaben 'yan
majalisu da aka gudanar a jihar Rivers.
Kakin rundunar Don Awunah ya ce binciken da ta
gudanar ya nuna cewa jami'an wadanda suka
hada da Sufeto Eyo Victor da Sajen Peter Ekpo
da Sajen Ogoni Goodluck sun yi harbi cikin
jama'a ba bisa ka'ida ba.
Sauran sun hada da Sajen Orji Nwoke da Sajen
Okpe Ezekiel da kuma Sajen Tanko Akor.
Ta kara da cewa sun aikata laifin ne ranar 10 ga
watan Disambar 2016 lokacin da suka bi tawagar
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, wajen dirar
mikiya a kan sakatariyar karamar hukumar
Fatakwal.
Sanarwar da Mista Awunah ya fitar ta ce jami'an
sun hana kai sakamako inda hukumar zabe ta
tanada daga rumfar zabe ta Umouha yayin zaben
cike gurbi da aka gudanar a ranar.
Ta kuma ce 'yan sandan sun nuna rashin biyayya
ga manyan jami'an 'yan sandan da ke wurin a
lokacin.
Rundunar ta 'yan sandan Najeriya ta kara da
cewa sai da aka gudanar da bincike a kan
lamarin kafin a dauki matakin korar jami'an.
Bayan ta sallame su daga aiki, rundunar ta ce za
ta gurfanar da su a gaban kuliya a karkashin
dokar zabe domin hakan ya zama darasi ga
sauran 'yan sanda.
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriyar, Idris
Ibrahim, ya ce a shirye rundunarsa ta ke domin
gudanar da aikinta yadda tsarin mulki ya tanada
lokacin zabe da kuma bayansa.
Zaben na jihar Rivers dai ya haifar da zafafan
kalamu tsakanin jami'iyyar PDP mai mulkin jihar
da kuma APC wacce ke adawa.
An kuma samu hasarar rayuka da dama a
rigingimun da aka yi masu alaka da zaben.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: An sallami 'yan sanda shida kan zaben Rivers"

Post a Comment